Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-14 16:55:28    
Gwamnatin Amurka na yin sauye-sauye ga shirinta na ceto kasuwannin hada-hadar kudi

cri

A ranar 12 ga wata, shugaban kwamitin bada hidimar harkokin kudi na majalisar wakilan Amurka, Barney Frank ya bayyana matukar rashin gamsuwarsa ga abin da Henry Paulson ya yi na yin fatali da shirin sayen kadarori daga bankuna.

A waje daya kuma, abin da ake faman ka-ce-na-ce a kai tsakanin majalisar dokoki da ma'aikatar kudin Amurka shi ne, bada tallafi ga manyan kamfanonin kera motoci uku na Amurka, wato GM, da Ford, gami da Chrysler. Paulson ya tsaya haikan kan kin samar da tallafi ga wadannan kamfanonin kera motoci. Ya ce, ko da yake masana'antun kera motoci na da muhimmiyar ma'ana ga tattalin arzikin Amurka, amma ya kamata a yi amfani da shirin dake kunshe da dala biliyan 700 domin ceto kasuwannin hada-hadar kudi, ba kamfanonin kera motoci ba.

Majalisar dokokin Amurka ta kara da cewa, ana rashin kyakkyawar kulawa kan yadda ake aiwatar da shirin ceto kasuwannin kudade. Majalisar dokokin ta bukaci da a kafa sassan sa ido a matakai daban-daban, ta kuma bukaci fadar White House da ta nada wani babban mai sa ido, domin sa ido kan yadda Henry Paulson ke yin amfani da ikonsa, da tasirin da matakan da ya dauka suke kawowa harkokin kudi da kasuwannin bada rance. Manazarta suna ganin cewar, a yanzu haka a Amurka, an zabi sabon shugaban kasar kwanakin baya ba da jimawa ba, kuma za'a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki nan ba da dadewa ba, shi ya sa watakila za'a dakatar da wannan sabon shiri har na tsawon 'yan watanni da dama.

Kafofin watsa labaru na ganin cewa, mai yiwuwa ne sabuwar gwamnatin Barack Obama za ta yi watsi da sabon shirin ciccibo kasuwannin hada-hadar kudi da ma'aikatar kudin Amurka ta bullo da shi. Kazalika kuma, shugaban kwamitin harkokin bankuna na majalisar dattijan Amurka Christopher Dodd ya ce, watakila ma za'a gano ainihin manufar tattalin arziki da Amurka ke bukata bayan da sabuwar gwamnatin kasar ta kama aiki.(Murtala)


1 2