Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-14 16:55:28    
Gwamnatin Amurka na yin sauye-sauye ga shirinta na ceto kasuwannin hada-hadar kudi

cri

Ministan kudi na Amurka, Henry Paulson ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, gwamnatin Amurka ta yanke shawarar yin fatali da shirin sayen kadarorin dake da matsala daga bankuna, za ta cigaba da zuba tsabar kudi cikin cibiyoyin hada-hadar kudi na kasar, haka kuma za ta kara bayar da rancen kudi ga dalibai, da samar da lamuni ga masu sayen motoci, da karin katunan bashi. Bayanin da Henry Paulson ya yi na nufin cewar, gwamnatin Amurka na yin sauye-sauye ga shirinta na ciccibo kasuwannin hada-hadar kudi a mataki na biyu, wato ta yi watsi da shirin sayen kadarorin dake da matsala daga hannun cibiyoyin kudade, abin da ta ba fifiko a halin yanzu shi ne taimakawa masu saye wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Yayin da Henry Paulson ke bayyana yadda ma'aikatar kudin Amurka za ta gudanar da harkokinta a mataki mai zuwa, ya ce, dalilin da ya sanya gwamnatin kasar ta yi fatali da tsohon shirinta shi ne sauye-sauyen halin da ake ciki a kasuwanni. Ya cigaba da bayyana cewar, aiwatar da shirin sayen kadarori daga bankuna na bukatar tsawon lokaci, amma sabon shirin gwamnati shi ne a sayi hannayen jari daga hannun bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi, ta yadda za'a bada kwarin-gwiwa ga bankunan Amurka da su farfado da harkokinta na bada rance yadda ya kamata, da kara bayar da rancen kudi ga masu saye.

Karkata hankali kan masu saye da ministan kudin Amurka Henry Paulson ya yi na alamanta cewa an cire kyallen da aka rufe kan shirin belin cibiyoyin kudaden Amurka a mataki na biyu. Kafofin watsa labarun Amurka sun nuna cewar, ma'aikatar kudin kasar ta yi ta kara maida hankalinta kan mawuyacin halin da masu saye ke ciki wajen rokon rancen kudi daga bankunan kasar. Paulson ya ce, ma'aikatarsa da asusun tarayyar Amurka na kokarin tsara wani shirin bada rance cikin hadin-gwiwa, domin bada kwarin-gwiwa ga masu saye da su sayi katin bashi.

Ko da yake ana cigaba da yin shawarwari kan sabon shiri, amma wasu manazarta sun fara tababar ko wannan shiri zai yi aiki, saboda aiwatar da shi na bukatar 'yan makonni da daloli sama da biliyan dari, amma zuwa yanzu, a cikin dala biliyan 350 da gwamnatin Amurka ke iya yin amfani da su, baya ga biliyan 250 domin sayen hannayen jarin bankuna, da biliyan 40 domin tabbatar da dorewar hamshaki mai bada inshora wato Kamfanin AIG na Amurka, akwai rarar kudin da yawanta ya kai dala biliyan 60 kawai. Idan ma'aikatar kudi tana fatan yin amfani da karin kudaden Amurka, ya kamata ta sake rokon amincewa daga majalisar dokokin kasar. Henry Paulson ya ce, har yanzu bai tsara ajandar rokon karin kudade daga majalisar dokoki ba.

1 2