Kamar yadda muka bayyana a baya, Panda dabba ce da ke fuskantar barazanar karewa, sabo da yanzu su 1590 ne kawai a duk duniya. Sabo da haka, har kullum gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci a wajen kiyaye su. Tun tuni a shekarun 1950, gwamnatin kasar Sin ta kafa shiyyar ba da kariya ga dabbobin Panda, wadda ta kasance ta farko a kasar, ya zuwa yanzu dai, gwamnatin kasar Sin ta rigaya ta kafa irin wadannan shiyyoyin da yawansu ya wuce 40 a duk kasar, ta kuma kafa hukumomin kula da ba su kariya a lardunan Sichuan da Shanxi da Gansu da aka fi samun yawan dabbobin, ta yadda kashi 95% na dabbobin na iya samun kariya kamar yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, a shekarar 1957, gwamnatin kasar Sin ta tsara dokar haramta farautarsu. A shekarar 1962 kuma, gwamnatin kasar Sin ta sanya panda a matsayin dabba mai matukar daraja da aka ba su kariya mafi kyau a kasar Sin.
Ban da wannan kuma, sabo da panda ba su iya hayayyafa sosai, su kan haifi 'ya'ya daya ko biyu ne kawai a kowace shekara. Sabo da haka, sassan da abin ya shafa na kasar Sin sun dade suna nazarin hanyar kimiyya da za a iya bi wajen kara yawansu. Bisa kokarin da aka yi, ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta daidaita manyan matsalolin da aka fuskanta a wannan fanni, har ma tana kan gaba a duniya.
Ban da wannan, bisa labarin da muka samu, an ce, a watan Maris na shekarar da muke ciki, bisa kirar masanan ilmin kimiyya na kasar Sin, masanan ilmin kimiyya na Canada da Birtaniya da Amurka da Denmark suka hada kansu suka fara aiki da shirin nazarin fasalin kwayoyin halitta na Panda, kuma kwanan baya, a birnin Shenzhen na kasar Sin, an kammala zana fasalin kwayoyin halitta na farko na Panda, wanda zai iya ba da taimako ta fannin ilmin kwayoyin halitta wajen ba da kariya ga dabbobin da ke bakin karewa. (Lubabatu) 1 2
|