Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-07 15:42:14    
Dabbobin Panda masu daraja a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Mu'azu Ibrahim, wanda ya fito daga garin Zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, malam Mu'azu ya ce, shin mene ne tarihin dabbar nan mai suna Panda da ke yankin Sichuan na kasar Sin? Shin kasar Sin ce kadai take da Panda a duniya? Shin ko Panda tana daga cikin nau'in dabbobin da aka sanya cikin barazanar karewa? In haka ne, wadanne hanyoyi ake bi domin tabbatar da rayukansu a doron kasa?

To, malam Mu'azu Ibrahim, ka yi mana tambayoyi da yawa dangane da dabbar Panda ta kasar Sin wadanda kuma ke da muhimmanci sosai, yanzu bari mu amsa su daya bayan daya.

Masu sauraro, al'ummar kasar Sin suna daukar Panda dabba ce mai daraja, sabo da Sin kadai take da dabbar a duniya, kuma a halin yanzu, akwai dabbobin Panda da yawansu ya kai 1590 ne kawai a duniya, shi ya sa ma iya cewa, suna cikin barazanar karewa.

Panda dabba ce da ke rayuwa a kasar Sin ne kawai, kuma yawancinsu suna zaune ne a duwatsu da ke kewayen lardin Sichuan na kasar Sin. Panda suna son cin gora, kuma gashinsu ya kan kasance baki da fari, wato jikinsu da jelarsu fari ne, a yayin da kunnuwa da idanu da kafafuwansu su kan kasance baki. Tsawon jikinsu ya kan kai kimanin centimita 120 zuwa 180, kuma nauyinsu ya kan kai kilogram 60 zuwa 110. Panda dabba ce mai ban sha'awa, kuma su kan sami karbuwa daga jama'a sabo da saukin kansu da kuma son jama'a.

Ban da wannan, a kan kira Panda kamar "dadaddiyar halitta", sabo da sun dade a doron kasa. Dabbobin Panda sun samo asalinsu ne daga wani irin dadadden naman daji da ke zaune a doron duniya yau da shekaru fiye da miliyan 60 da suka wuce, kuma suna da dangantaka da dabbar bear da damisa na zamanin yanzu. Sa'an nan, yau da shekaru kimanin dubu 10 da suka wuce, dabbobin panda da muke gani a yau suka bayyana a doron duniya.


1 2