Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-05 16:08:18    
Jama'ar kasar Kenya suna fama da tsadar man fetur

cri

Saboda haka, a kwanakin baya, Mr. Kibaki shugaban kasar Kenya ya kalubalanci kamfanin man fetur na kasar Kenya ya rage farashin man fetur tun da wuri domin tinkarar matsalar raguwar darajar kudi. Ya ce, farashin man fetur na kasuwar duniya ya riga ya ragu, ya kamata a rage farashin man fetur nan da nan domin moriyar jama'a.

Ban da haka kuma, a kwanakin baya, Mr. Mulun ministan makamashi na kasar Kenya ya yi kira ga jama'ar kasar Kenya da su kaurace wa 'yan kasuwar man fetur na kasashen waje domin kalubalantar da su rage farashin man fetur. Ya ce, ma'aikatar makamashi ta kasar Kenya ta riga ta daina saye man fetur daga wadannan 'yan kasuwa na kasashen waje, maimakon haka tana sayen man fetur daga kamfanin man fetur na kasar Kenya.

Amma, farashin man fetur da kamfanin kasar Kenya yake sayarwa ba shi da rahusa ba. musalin a kwanakin baya, farashin man fetur da kamfanin Total na kasar Faransa ke sayarwa a kasar Kenya ya kai Shilling din Kenya fiye da 101.50 zuwa fiye da 108.50 na ko wace lita, amma farashin man fetur da kamfanin man fetur na kasar Kenya ya sayar ya kai Shilling din Kenya 101.50 zuwa fiye da 104.90 na ko wace lita.

A kwanakin baya, kwamitin kula da makamashi na kasar Kenya ya yi kira ga kamfannonin man fetur da su rage farashin man fetur da Shilling na Kenya 8.49 kan ko wace lita, ta haka domin rage nauyin zaman rayuwar jama'a. Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Kenya tana kokarin neman sayen danyen man fetur daga kasar Sudan da farashi mai rahusa, a watan da ya gabata, kasashen biyu sun riga sun daddale takardar fahimtar juna. Idan an fara gudanar da wannan shiri, kasar Kenya za ta saya danyen man fetur ganga dubu 500 daga kasar Sudan, wannan zai rage farashin man fetur na kasar Kenya.


1 2