Mr. Peter wanda shekarunsa sun kai 48 da haihuwa, wani ma'aikacin tsabtace muhalli ne a Nairobi babban birnin kasar Kenya, yana da yara guda hudu, kullum suna fama da karancin kudi, suna kaffa-kaffa. Mr. Peter ya ce, akwai nisa daga gidansa zuwa wurin aikinsa, yana bukatar lokaci kamar mintoci 20 dan zuwa wurin aiki cikin bus, amma kullum yana zuwa aiki da kafa inda ya kan ci lokacin fiye da awa guda domin ya yi tattalin kudin biyan bus na Shilling din Kenya 50, kusan dolar Amurka guda.
Ya ce, saboda karuwar kudin man fetur, yawan kudin da ya kan kashe kan bus ya karu da Shilling din Kenya 30 a cikin shekaru biyu da suka wuce, yanzu mutane da yawa na kasar Kenya suna zuwa aiki ne da kafa.
Matsakaicin yawan kudin da ko wane mutumin kasar Kenya ya samu daga wajen samar da kayayyaki ya kai dolar Amurka 660. Amma, man fetur yana da tsada sosai a kasar Kenya da ke gabashin Afirka. Man fetur da ake sayar wa a Nairobi ya kai fiye da Shilling din Kenya 100 na ko wace lita.
Karuwar farashin makamashi ta haifar da matsala ga gwamnati wajen tinkrar matsalar raguwar darajar kudi. A watan Mayu na shekarar da muke ciki, yawan raguwar darajar kudi ya kai kashi 31.5 cikin kashi 100, wannan ya zama matsayi mafi koli a cikin shekaru 10 da suka wuce. Ko da yake yawan raguwar darajar kudi ya ragu zuwa kashi 26.5 cikin kashi 100 a watan Yuli, amma ya sake karuwa zuwa kashi 27.6 cikin kashi 100 a watan Agusta. Manyan dalilan da suka haddasa haka su ne karuwar farashin man fetur da na wutar lantarki, wannan ya haifar da damuwa sosai ga jama'ar kasar Kenya.
1 2
|