Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:49:31    
Fasahar yin amfani da hasken rana ta zama wata gada ce wajen hadin gwiwa tsakanin lardin Gansu da waje

cri

Madam Zhang Lanying, mataimakiyar shugaban cibiyar nazari kan makamashin halitta ta lardin Gansu ta bayyana cewa, cibiyar fasahar yin amfani da hasken rana da za a kammala kafa ta a karshen shekarar da muke ciki za ta samar da kayayyakin yin amfani da hasken rana da kuma shirye-shiryen bunkasuwa daban daban bisa bambancin kasa da kasa. Kuma ta kara da cewa:

"A cikin kwasa-kwasanmu na horaswa, za a kebe lokuta wajen yin cudanyar fasaha domin biyan bukatun kasashe daban daban. Idan ake da burin hadin gwiwa tare da mu, to muna iya ci gaba da yin shawarwari. Ala misali, wasu kasashe suna karancin kwal, suna bukatar kayayyakin dafa abinci na yin amfani da hasken rana, to za mu samar da kwas din horaswa gare su kan kayayyakin dafa abinci na yin amfani da hasken rana. Wasu kasashe kuma suna karancin wutar lantarki, ba su da tsarin samar da wutar lantarki, to za mu samar da kwas din horaswa gare su kan fasahar yin amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki."

Kuma Madam Zhang ta bayyana cewa, lardin Gansu zai ci gaba da kara ayyukan horaswa na fasahar yin amfani da hasken rana domin samar da taimako ga waje, da kuma inganta hadin kan tattalin arziki da taimakon juna tsakanin lardin da sauran kasashe da yankuna ta hanyoyin cudanyar labarai da musanyar fasahohi da kuma raya kasuwanni, ta yadda fasahar yin amfani da hasken rana za ta zama daya daga cikin gadoji wajen yin cudanya tsakanin lardin Gansu har kasar Sin da kasashen waje.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)


1 2