A karshen watan Nuwamba na shekara ta 2007, an kaddamar da kafa cibiyar sa kaimi ga musanyar fasahar yin amfani da hasken rana tsakanin kasa da kasa ta kungiyar raya masana'antu ta MDD a birnin Lanzhou, hedkwatar lardin Gansu na kasar Sin. Kafin wannan, har kullum kasashen duniya suna muhawara kan inda ya kamata a kafa cibiyar. To don me a karshe dai aka zabi lardin Gansu na kasar Sin wajen kafa cibiyar? Xi Wenhua, shugaban cibiyar kuma shugaban cibiyar nazari kan makamashin halitta ta lardin Gansu ya bayyana cewa:
"Dalilin da ya sa aka kafa wannan kungiyar kasa da kasa a lardin Gansu shi ne sabo da lardin ba ya samun ci gaba, inda ke kasancewa da gurbacewar muhalli, sai dai aka yi haka ne domin za a iya sa kaimi ga kyautatuwar muhallin wurin da canja ra'ayin mazaunan wurin da kuma samun bunkasuwar tattalin arzikinsa."
Bisa yarjejeniyar da gwamnatin kasar Sin da kungiyar raya masana'antu ta MDD suka daddale, an kafa cibiyar fasahar yin amfani da hasken rana bisa tushen cibiyar nazari kan makamashin halitta ta lardin Gansu, wadda ita ce hukuma ta farko ta kasar Sin wajen yin nazari kan hasken rana daga manyan fannoni. Ya zuwa yanzu, cibiyar ta riga ta kirkiri fasahohi iri fiye da 130 wajen yin amfani da hasken rana, kuma fasahohi 20 daga cikinsu sun samu lambobin yabo na matsayi na kasa da na lardi. Xi Wenhua ya bayyana cewa, shirya kwasa kwasan horaswa tsakanin kasa da kasa cikin dogon lokaci da kuma samun yabo sakamakon yin haka su ma muhimman dalilai ne da suka sanya lardin Gansu ya samu wannan aiki. Kuma ya kara da cewa:
"Ya zuwa yanzu mun riga mun horar da kwararrun da ke rike da fasahohin musamman da jami'an gwamnatoci da abin ya shafa da yawansu ya kai kimanin 700, wadanda suka zo daga kasashe 96 na nahiyoyi biyar. A waje daya kuma mun gudanar da dimbin ayyukan hadin kain tsakanin bangarori daban daban, ciki har da ayyukanmu na samar da taimako ga waje, wadanda suka taka muhimmiyar rawa a duniya."
1 2
|