Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-30 14:50:59    
Girgizar kasa a Pakistan

cri

Ko da yake yanzu gwamnatin Pakistan na iyakacin kokarin gudanar da ayyukan agaji, amma duk da haka, ana fuskantar manyan matsaloli biyu. Na farko, sabo da yawancin gidajen kauyukan wurin sun lalace sakamakon girgizar kasar, ga shi kuma akwai sanyi sosai a wurin cikin dare, har kasa da digiri sifiri, don haka mazaunan wurin na shan wuya sosai da dare. A yankin Ziarat da ya fi fama da bala'in, ko da yake gwamnatin Pakistan ta riga ta samar musu da tantuna 3000 a ran nan, amma jami'an wurin na bukatar gwamnati ta kara samar da tantuna dubu 10 tare kuma da kayayyakin dumama jiki cikin sauri. Na biyu kuwa, ana ci gaba da fama da tsilla-tsillar aukuwar girgizar kasa. Zaizayewar duwatsu na zama sabuwar barazana a gaban jama'a da kuma masu aikin agaji.

Girgizar kasa ta kuma jawo hankula da tausayi daga gamayyar kasa da kasa. Bayan aukuwarta, shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao da firaminista Wen Jiabao na kasar sun nuna jaje ga gwamnatin Pakistan da jama'arta, sun kuma taya su alhini game da rashin wadanda suka mutu. Amurka da dai sauran kasashe da kungiyoyin duniya su ma sun bayyana burinsu na samar da gudummawa ga Pakistan. Abin da ya kamata mu ambata shi ne, gwamnatin Indiya ta mayar da martani cikin sauri, ba da jimawa ba bayan aukuwar girgizar kasar, sai ta yi shelar ba da dukan taimakon da ya yiwu ga Pakistan. Yanzu kungiyar Red Cross ta riga ta aika da rukunoni biyu zuwa yankunan da bala'in ya shafa, don su kimanta halin da ake ciki da kuma abubuwan da jama'ar wurin ke bukata. A karkashin jagorancin gwamnatin Pakistan kuma bisa taimakon da gamayyar kasa da kasa ke bayarwa, muna da imanin cewa, jama'ar Pakistan da bala'in ya galabaitar da su za su iya haye wahalhalu da ke gabansu, su farfado da gidajensu.(Lubabatu)


1 2