Ranar 29 ga wata, an yi girgizar kasa mai tsanani da karfinta ya kai digiri 6.5 bisa ma'aunin Richter a lardin Baluchistan da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan, wanda ya janyo wa jama'a dimbin hasarori. Bayan aukuwarta, gwamnatin Pakistan ta yi iyakacin kokarin yaki da girgizar kasar da kuma ba da agaji.
A ran nan da sassafe, da misalin karfe hudu da minti 33, jama'a sun farka daga barci cikin firgici sakamakon wata girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 5. Bayan kimanin minti 40, wata girgizar kasa mai karin tsanani ta sake afkawa, wadda har karfinta ya kai digiri 6.5.
Girgizar kasar ta janyo wa mazaunan wurin dimbin hasarori. A cewar wani jami'in wurin, akwai mutane kimanin dubu 46 da ke da zama a yankunan da girgizar kasar ta shafa, kuma kauyuka a kalla 8 sun lalace sosai. A ran nan, Farooq Ahmed Khan, shugaban hukumar kula da bala'u ta Pakistan, ya ce, an riga an tabbatar da mutuwar mutane 115 sakamakon girgizar kasar, tare kuma da wasu 300 da suka ji raunuka. Amma sabo da dimbin mutane na karkashin kufayi, don haka adadin mutuwar mutane na iya kara karuwa.
Girgizar kasar ta jawo hankulan manyan shugabannin Pakistan sosai. Shugaban kasar, Asif Ali Zardari tare kuma da firaminista Yousuf Raza Gilani wanda ke ziyara a kasar Turkiya, dukansu sun nuna juyayi ga wadanda suka mutu a girgizar kasar, sun kuma umurci gwamnatin tarayya da hukumar wurin da su yi iyakacin kokarin ba da agaji ga wadanda bala'in ya galabaitar da su.
Bayan aukuwar girgizar kasar, nan da nan hukumar wurin da sassan kiwon lafiya suka fara gudanar da ayyukan agaji, sun kafa wasu tantuna a yankunan da girgizar kasar ta shafa, don su zama asibiti na wucin gadi, su yi wa wadanda suka ji raunuka masu tsanani jiyya. Sauran mutanen da ba su ji rauni sosai ba, an kai su asibitocin da ke kusa. Ban da wannan, rundunar sojan Pakistan ta aika da jiragen sama masu saukar ungulu 12 zuwa yankunan da bala'in ya shafa. Yanzu ana gudanar da ayyukan agaji cikin gaggawa.
1 2
|