Game da daftarin dokar tabbatar da ingancin abinci, mataimakin darektan kwamitin dokokin shari'a na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Liu Xirong ya gaya mana cewa,
'A halin yanzu dai, ba a kayyade yadda ake yin amfani da kayayyakin da ake hadawa cikin abinci ba, wannan dai ya zama wata babbar matsala da ke haddasawa abinci rashin inganci. Wannan daftarin dokar tabbatar da ingancin abinci ta kayyade sosai a wannan fanni.'
A farkon wa'adi da aka shigar da dokar tabbatar da ingancin abinci cikin yunkurin kafa dokokin shari'a a karshen shekarar da ta wuce, darektan ofishin dokoki na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mr. Cao Kangtai ya ce,
'A halin yanzu dai, tsarin kula da ingancin abinci, da na sa ido kan ingancin abinci na bukatar kyautatuwa, haka kuma babu karfi sosai wajen yanke hukunci kan ayyukan karya doka wajen kera abinci rashin inganci. Haka kuma ba a iya samu hukumomin kula da ingancin abinci da yadda suke kwarewa yadda ya kamata ba. Sabo da haka ne, ake shirin kafa dokar tabbatar da ingancin abinci domin daidaita wadannan matsalolin da muka ambata.'(Danladi) 1 2
|