Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-24 17:38:34    
A karo na uku, kasar Sin ta dudduba daftarin dokar tabbatar da ingancin abinci, domin inganta gina tsarin sa ido da kula da ingancin abinci

cri

Bayan faruwar lamarin matsalar garin madara da aka yi domin jarirai da kananan yara a watan da ya gabata, kasar Sin ta dinga daukar manyan matakai wajen daidaita matsalolin da ke shafar ingancin abinci. Game da matsalolin da aka gano, cikin sauri ne dokar tabbatar da ingancin abinci da ake shirin tsarawa a halin yanzu ta kayyade ka'idojin maida abinci, da bincike na dole, haka kuma ta karfafa sa ido da kula da kayayyakin da ake hadawa cikin abinci. Bayan da aka koyi darasi daga lamarin matsalar garin madara, da kuma yin gyare gyare a fannoni da dama, a karo na uku, an gabatar da daftarin dokar tabbatar da ingancin abinci ga hukumar kafa dokoki wato kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin domin ya dudduba shi.

Bayan faruwar lamarin matsalar garin madara, sau da yawa, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya ce, ya kamata a koyi darasi da inganta kafa tsari mai kyau. Ya ce,

'Wani abun da ya fi muhimmanci gare mu shi ne, mu koyi darasa daga wannan lamari, ya kamata mu inganta kafa tsari mai kyau, kuma mu mai da hankulanmu sosai wajen sa ido da bincike kan ko wane bangaren aikin kawo albarka tun daga fannin hadawa da kuma bayan hakan.'


1 2