Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-21 18:31:30    
Shugabannin manyan addinai biyar na kasar Sin suna son ba da taimakonsu wajen tabbatar da zaman lafiya a Asiya da kuma duniya baki daya

cri

Sin kasa ce da ke da mabiyan addinai da dama, kuma muhimman addinan da ake bi sun hada da Buddah da Taoism da musulunci da Katolika da kuma Kiristanci. Kasar Sin na aiwatar da manufar tabbatar da 'yancin jama'a na bin addinin da aka ga dama. Yanzu akwai mabiyan addinai da yawansu ya wuce miliyan 100 a kasar Sin, tare kuma da wuraren ibada fiye da dubu 85. A game da yadda addinai daban daban ke bunkasa a kasar Sin, Madam Gao Ying, mataimakiyar shugaban kungiyar addinin Kiristanci ta kasar Sin, ta ce,"Idan mun duba halin da ake ciki gaba daya, za mu gane cewa, mabiya addinai suna da iyakacin 'yancin bin addinansu. Addinai daban daban na zauna lafiya da juna a kasar Sin. Muna son ba da namu taimako wajen tabbatar da jituwa tsakanin addinai a Asiya."

Manyan addinai guda biyar na kasar Sin dukansu suna yada manufar zaman lafiya da zaman jituwa. Amma duk da haka, yake-yake da ta'addanci da nuna karfin tuwo da bambancin da ke tsakanin matalauta da masu arziki tare kuma da arangama da juna a tsakanin kasashe da kabilu da kuma addinai daban daban, sun kawo babban kalubale a gaban zaman lafiya. Mr.Chen Guangyuan, shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin yana ganin cewa,"Tabbatar da tuntubar juna da fahimtar juna a tsakanin addinai daban daban na da muhimmanci sosai wajen daidaita rikice-rikice iri iri. Shawarwari wata muhimmiyar hanya ce wajen hana rikici. Ta hanyar yin shawarwari, za a kara fahimtar juna, kuma hakan zai iya tabbatar da zaman lafiya."

Xuecheng, mataimakin shugaban kungiyar addinin Buddah ta kasar Sin ya ce, dalilin da ya sa bangaren addinai na kasar Sin suka halarci taron shi ne don tabbatar da zaman lafiya a Asiya da kuma duniya baki daya, ya ce, "Bisa taken taron, mu wadanda muka zo daga bangaren addinai na Asiya mun tattauna, mun karfafa fahimtarmu dangane da zaman lafiya, kuma za mu koyar da mabiyan addinanmu, ta yadda za mu ba da taimako ga samar da zaman lafiya. Kamata ya yi mu sanya addinai su taka rawa mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya a Asiya da ma duniya baki daya, a maimakon su zama sanadiyyar rikici."(Lubabatu)


1 2