Yau ne aka rufe taron mabiya addinai daban daban na Asiya a karo na 7 domin samar da zaman lafiya, a birnin Manila, babban birnin kasar Philippines. An dai fara taron ne a ran 17 ga wata, kuma a lokacin taron, shugabannin manyan addinai guda biyar na kasar Sin suka bayyana wa wakilinmu cewa, suna son ba da nasu taimako wajen cimma burin tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Asiya da kuma jituwa a duk duniya.
Taron na da taken "samar da zaman lafiya a Asiya", kuma wakilai fiye da 300 da suka zo daga kasashe da yankuna kimanin 30 sun hallara. Kwamitin zaman lafiya na addinai daban aban na kasar Sin shi ma ya tura wata tawagar da ke kunshe da wakilai 28 zuwa wajen taron.
Shugaban tawagar kuma mataimakin shugaban kwamitin kishin kasa na addinin katolika na kasar Sin, Mr.Liu Bonian yana ganin cewa, wadanda suka zo daga bangaren addinai na kasar Sin sun yi kokarin ba da ra'ayoyinsu dangane da samar da zaman lafiya a Asiya, wannan ya dace da manufar kwamitin zaman lafiya na addinan kasar Sin, ya ce,"A kasar Sin, addinai daban daban na zama daidai wa daida da juna, ba su taba samun rikici a tsakaninsu ba. Kwamitin zaman lafiya na addinan kasar Sin da ke kunshe da wakilan manyan addinai guda biyar na kasar Sin yana bin manufar sada zumunta da zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa, kuma yana yada kyakkyawar al'adar kishin kasa da son zaman lafiya, kuma yana son bunkasa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsa da kungiyoyin addinai na samar da zaman lafiya na duniya da yankuna da kuma na kasashe daban daban, don kiyaye dinkuwar kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya da cigaba a duniya."
1 2
|