Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-21 15:24:38    
Filin wasa na sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Baya ga yin amfani da na'urorinta da kuma kashe kudin Hong Kong fiye da miliyan 800 wajen yin kwaskwarima da fadada filayen wasa, hadaddiyar kungiyar tseren dawaki ta Hong Kong za ta kuma ba da goyon baya ta fuskar guzuri wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da ta nakasassu a fannoni daban daban a matsayin wata kwararriya, kamar su samar da motocin yin jigilar dawaki da asibitocin dawaki da tashoshin bincike a filin wasa da dawaki a Beijing.

A watan Agusta na shekarar bara, an sami nasarar shirya gasar shirye-shirye 3 na wasa da dawaki ta kasa da kasa a filin wasa na sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a Hong Kong. A matsayinta na daya daga cikin gasannin yin gwajin filayen wasa wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, gasar da aka yi a shekarar bara ta yi wa filin wasa na sukuwar dawaki a Hong Kong gwaji ta fuskar wurin gasa da na'urori da aikin kiwo lafiyar dawaki da tsaron lafiyar mutane da lafiyar dawaki da sufuri da aikin sadarwa da kuma matsayin ma'aikata wajen ba da hidima. Gasar ta sami amincewa daga hadaddiyar kungiyar wasan Olympic ta kasa da kasa da hadaddiyar kungiyar wasa na sukuwar dawaki ta kasa da kasa. Bugu da kari kuma, kwamitin wasan Olympic na Hong Kong da hadaddiyar kungiyar tseren dawaki ta Hong Kong sun tattara ingantattun fasahohin shirya gasanni. Babu tantama wannan zai dasa harsashi mai kyau wajen samun nasarar shirin wasa na sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing.


1 2 3