Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-21 15:24:38    
Filin wasa na sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Masu karatu, kowa ya sani cewa, za a shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara. Birane 6 na kasar Sin sun ba da taimako wajen shirya wannan muhimmiyar gasa. Za a yi shirin wasa na sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing da na gasar wasannin Olympic ta Beijing ta nakasassu a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Yanzu an kammala gina galibin filayen wasa da na'urorin aikin horaswa domin wannan shiri.

Bisa shirin da aka tsara, za a yi shirin wasa sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing a filayen wasa 2, wato za a yi shirin ketare shinge da shirin wasa sukuwar dawaki tare da kida a filin wasa sukuwar dawaki na Shatian. Sa'an nan kuma, za a yi sashen gudun fanfalaki kan dawaki na shirin wasa sukuwar dawaki na tsawon kwanaki 3 a filin wasa ta ketare shinge da gudu na dogon zango kan dawaki na Shangshui. A cikin wadannan filayen wasa 2, an kuma samar da isassun na'urorin da abin ya shafa.


1 2 3