Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-15 16:05:24    
An bude wa jama'a kofofin gidajen baje koli na kasar Sin ba tare da biyan kudi ba

cri

Shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi na birnin Beijing Mr Kong Fanzhi ya bayyana cewa, damuwarmu ita ce, mutane masu yawan gaske za su kai ziyara a gidajen baje koli, wannan zai kawo cikas ga muhallin gidajen, kuma kara karuwar mutane da yawa cikin gajeren lokaci zai kawo illa ga tsaron kai na 'yan kallo, saboda haka mun tsara hanyoyin da za a bi ta hanyar yin rajista kafin ziyararsu.

Kafin bude wa jama'a kofofin gidajen baje koli ba tare da biyan kudi ba, birnin Beijing ya soma horar da mutane wajen maganin faruwar al'amarin ko ta kwana, sa'anan kuma gidajen baje koli daban daban su ma sun bayar da lambobin wayarsu ga jama'a don su yi rajista sunayensu kafin ziyararsu a wadannan gidaje.

Wani dalibin da ya zo daga kasar Britaniya ya gaya wa manema labaru cewa, na ji abin nan da aka yi na da kyau sosai, za a iya kallon abubuwa da yawa a wuraren ba tare da biyan kudi ba, wannan zai ba da taimako ga mutanen da suka zo daga kasashen waje wajen kara fahimtar al'adun kasar Sin.

A lokacin yin wasannin Olimpic na shekarar 2008, watakila masu yawon shakatawa na kasashen waje da wasu 'yan wasan motsa jiki za su shiga gidajen baje koli na kasar Sin iri iri don kara fahimtar al'adun kasar Sin. Shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi ta birnin Beijing Mr Kong Fanzhi ya bayyana cewa, babu matsala da za a samu in bakin kasashen waje da masu yawon shakatawa na kasar Sin za su kai ziyara a gidajen baje koli a sa'i daya, duk saboda mun amince da matakan da aka dauka na tsaron kai, kuma masu kai ziyara suna da halin kirki, mun amince cewa, kowa zai yi gamsuwwarsu a lokacin da suke yin ziyara a gidajen baje koli. bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an bayyana cewa, yawan mutanen da suka kai ziyara a gidajen baje koli ya karu da yawa bisa na da, saboda mutane sai kara yawa suke yi, shi ya sa an sami cikas wajen kiyaye kayayyakin tarihi, wadannan matsaloli sun riga sun jawo hankulan sassan da abin ya shafa, gidajen baje koli da yawa sun riga sun tsara kuduri na kayyade yawan mutanen da za su shiga cikin gidajen a kowace rana da kuma gyara abubuwan da suke kare kayayyakin tarihi, ta hakan za a iya biyan bukatun shigar da jama'a cikin gidajen da kuma kare ingancin kayayyakin tarihi. (Halima)


1 2