Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-15 16:05:24    
An bude wa jama'a kofofin gidajen baje koli na kasar Sin ba tare da biyan kudi ba

cri

A cikin dogon lokaci, gidajen baje koli na kasar Sin sun bude wa kofofinsu ga jama'a tare da biyan kudi, amma yanzu, an riga an gyara halin nan, wato in aka shiga wasu gidajen baje koli , to ba za a biya kudi ba. Wannan ne matakin da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta dauka na samar wa jama'a saukin shiga gidajen. Ya zuwa ranar 1 ga watan Afril, gidajen baje koli masu samar wa jama'a alheri da gidajen tunawa na kasar Sin da yawansu ya kai 600 sun bude wa jama'a kofofinsu ba tare da biyan kudi ba, ya zuwa shekara mai zuwa, yawansu zai kara karuwa zuwa 1400.

Gwamnatocin matakai daban daban na kasar Sin sun ware kudade da yawa don nuna goyon baya ga gidajen baje koli wajen bude kofofinsu ga jama'a ba tare da biyan kudi ba da kuma biyan bukatun da jama'a ke kara yi a fannin al'adu a kowace rana.

Kullum gidajen baje koli na kasar Sin suna bude wa 'yan makarantun firamare da sakandare da tsofaffi kofofinsu ba tare da biyan kudi ba. A watan Maris na shekarar 2007, birnin Shenzhen mai wadata sosai da ke kudancin kasar Sin ya fara bude kofofin gidajen baje koli nasa ga jama'a ba are da biyan kudi ba, a ranar 6 ga watan Nuwamba na wannan shekara kuma, lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin shi ma ya shelanta cewa, zai bude wa jama'a gidajen baje koli nasa ga jama'a ba tare da biyan kudi ba har abada. Abin nan da aka yi ya sami karbuwa sosai daga jama'a. Wani ma'aikaci ya gaya wa manema labaru cewa, a da, kudin da za a biya domin shiga gidajen baje koli na da tsada, amma yanzu, ba a biya kudin shiga ba, to wannan ya samar wa 'ya'yan iyalan da suke fama da talauci damar more albarkatan jama'a bisa zaman daidaici, muna maraba da wannan sosai. Mataimakin ministan al'adun kasar Sin Mr Zhou Heping ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya da na wurare daban daban na kasar Sin dukkansu sun ware kudaden musamman da yawa domin bude kofofin gidajen baje koli ga jama'a don ba da tabbaci ga jama'a wajen samun ikonsu na al'adu ta hanyoyi daban daban. Ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya ta ware kudin da yawansu ya kai miliyan 1200, saboda haka a kai a kai ne gidajen baje koli na wurare daban daban suka bude kofofinsu ga jama'a ba tare da biyan kudi ba.Alal misali, lardin Hubei ya ware kudin da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 30 a kowace shekara, birnin Beijing ya ware kudin da yawansu ya kai Yuan miliyan 100 ko fiye a kowace shekara domin shigar da jama'a cikin gidajen baje koli ba tare da biyan kudi ba. A shekarar da muke ciki zuwa shekara mai zuwa, dukkan gidajen baje koli na kasar Sin za su bude kofofinsu ga jama'a ba tare da biyan kudi ba. Mataimakin shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi na kasar Sin Mr Zhang Bai ya bayyana cewa, ya kamata a kara daga matsayin gidajen baje koki da karfinsu wajen samar da hidima. Yanzu mutane da yawa za su je kallon gidajen baje koli, wannan ne ba daya da na da ba, saboda haka dole ne a kara ba da tabbaci ga mutane wajen tsaron kai dangane da gine-gine da sauransu.


1 2