Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-15 17:03:49    
Idan yara suka samu karfin zuciya, to za su fi samun lafiyar jiki bayan da su girma

cri

A shekara ta 2000, manazarta na kasar Birtaniya sun sake yin ziyara ga yaran da aka taba gudanar da bincike gare su, kuma sun tuntubi mutane 7551 daga cikinsu, da kuma fahimtar halin da suke ciki a fannonin jiki da kuma tunani ta takardun tambayoyi. Sakamakon takardun ya shaida cewa, yara mai shekaru 10 da haihuwa da rayuwarsu suka dogara bisa jagorancin dalilan ciki sun fi gamsuwa da lafiyar jikinsu lokacin da shekarunsu ya kai 30 da haihuwa, haka kuma yiyuwar kamuwa da hauhawar jini da cutar bakin ciki gare su ba ta kai matsakacin matsayi ba.

Katharine Gail, manazarciya ta farko mai kula da wannan bincike kuma furofesar jami'ar Southampton ta bayyana cewa, dalilin da ya sa yaran da rayuwarsu suka dogara bisa jagorancin dalilan ciki suka fi lafiya a wasu fannoni bayan da suka girma shi ne sabo da tun lokacin yarantakarsu, sun fi nuna karfin zukatansu a fannin fahimtar samun wani sakamako bisa harkokin da suke tafiyar da kansu, kuma irin wadannan mutane sun fi dora muhimmanci kan mutuncinsu da kuma kara kwarin gwiwarsu wajen samun kyakkyawar dabi'a.

Ban da wannan kuma Madam Gail ta nuna cewa, abin da ke jagorancin rayuwar mutum yana da nasaba da zaman rayuwarsa na lokacin yarantakarsa, kamar yin cudanya tare da iyaye da dai sauransu. Wasu iyaye su kan karfafa zukatan yaransu wajen yin tunani bisa karfin kansu, da kuma tallafa wa yaransu wajen fahimtar dangantakar da ke tsakanin aikatawa da sakamako, ta haka yaransu sun fi saukin samun halin musamman na abin da ke jagorancin rayuwar mutum bisa dalilan ciki.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya. (Kande Gao)


1 2