Kamar yadda Hausawa su kan ce, "Yaro wata rana uba ne", a 'yan kwanakin nan da suka gabata, manazarta na kasar Birtaniya sun shaida cewa, lalle wannan magana ta yi daidai sosai, watakila hauhawar jini da cutar bakin ciki da dai sauran cututtukan da a kan kamu da su bayan girma suna da nasaba da tunani a lokacin yarantakarsu.
Manazarta na jami'ar Southampton da ta Glasgow da kuma ta Edinburgh ta kasar Birtaniya sun ba da rahoto a kan mujallar ilmin likitanci kan jiki da tunani ta kasar Amurka, cewa sun gudanar da wani bincike ga yara dubu 11 da shekarunsu ya kai 10 da haihuwa ta hanyar takardun tambayoyi a shekara ta 1980 domin su amsa tambayoyin kan cewa, ko su samu maki mai kyau wajen karatu bisa sa'a da suka taka kawai, ko su kan ganin cewa, ko da yake suka yi kokari sosai wajen karatu, amma ba shi da amfani, ta yadda za a iya tabbatar da cewa, ko rayuwarsu suna dogara bisa jagorancin dalilan waje ko bisa jagorancin dalilan ciki.
Ma'anar abin da ke jagorancin rayuwar mutum ita ce karfin da mutane suke iya fahimta wajen jagorancin rayuwarsu bisa amfanin tunani da kuma muhallin waje, wanda ke kunshe da fahimtar hanyoyin tafiyar da harkoki da kuma daukar alhakin sakamakonsu da dai sauransu. Haka kuma abin da ke jagorancin rayuwar mutum yana da iri biyu, wato bisa dalilan ciki da kuma bisa dalilan waje. Mutanen da ke cikin rukunin farko suna ganin cewa, sun samu wani sakamako ne bisa dalilan da su kansu suka haddasa, kamar kwarewarsu da kuma kokarinsu. Kuma mutanen da ke cikin rukuni na biyu suna ganin cewa, muhalli da sa'a da dai sauran dalilan waje su ne su kan sanya a samu wani sakamako. Haka kuma mutanen da rayuwarsu ke dogara bisa jagorancin dalilan ciki sun fi samun karfin zukatansu.
To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yi muku wannan bayani kan cewa, idan yara suka samu karfin zuciya, to za su fi samun lafiyar jiki bayan da su girma.
1 2
|