Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-15 09:22:41    
An yi zama na farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya a Beijing

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, kasar Sin ta shirya gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu cikin cikakkiyar nasara, yanzu dai za ta ci gaba da zama kasa mai shirya gasar wasa kwakwalwa ta duniya, game da wannan, mataimakiyar shugabar kwamitin wasannin Olympic na kasar Sin Xiao Min tana ganin cewa, an zabi kasar Sin da ta shirya zama na farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya, wannan ya shaida mana cewa, kwamitin wasannin Olympic na duniya da kawancen wasa kwakwalwa na duniya sun yarda da cewa, tabbas ne kasar Sin za ta yi kokari kuma za ta ci nasara. Ban da wannan kuma, wannan shi ma ya nuna mana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan batun yalwata wasannin motsa jiki daga duk fannoni. Madam Xiao Min ta ce, "Mun shirya gasar wasa kwakwalwa ta duniya bayan gasar wasannin Olympic, wannan ya nuna mana cewa, wasannin yin takara da wasannin motsa jikin jama'a suna samun bunkasuwa tare kuma a lokaci daya a kasar Sin, kuma wasa kwakwalwa yana da muhimmanci a cikin sha'anin wasan motsa jiki na kasar Sin."

A halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da gasar wasa kwakwalwa ta duniya lami lafiya, bayan gasannin da aka shirya a cikin 'yan kwanakin da suka shige, 'yan wasa da masu horaswar da suka zo daga wurare daban daban na duk fadin duniya sun nuna babban yabo ga matsayin gasa da aikin shirya gasar da kasar Sin ke yi.

Yayin da shugabar hukumar kula da harkar wasan darar chess ta duniya Shigeno Yuki take takalo magana kan batu game da kasar Sin ta samun iznin shirya zama na farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya, ta ce, "Ya yi kyau kwarai! Na hakkake cewa, dukkan 'yan wasa suna farin cikin shiga gasar, ana yin gasa ana sada zumunta kuma ana jin dadin zaman rayuwa a kasar Sin. Lallai kasar Sin kasa ce mai gwanintar wasan darar chess. Mun tarar da cewa, gaba daya 'yan wasan darar chess dari 4 sun shiga gasar da ake shirya musu, Kowa na jin dadin gasar, a nan kuma bari in nuna babbar godiya ga kwamitin shirya gasar na kasar Sin saboda matukar kokarin da yake yi."

Adam Hicman 'dan wasan karta ne daga kasar Ingila, ya gaya mana cewa, a da bai taba zuwa kasar Sin ba, wannan ne karo na farko da ya sauka a kasar Sin, shi ya sa yana yin farin ciki sosai, kuma yana jin dadin zaman rayuwa a kasar Sin kwarai da gaske, ya ce, "Ban taba zuwa kasar Sin ba, saboda haka na yi sha'awa da kuma mamaki, 'yan wasa daga wurare daban daban sun zo wuri daya sun yi takara, kowane 'dan wasa yana da al'adarsa. Kasar Sin ta yi kokari, kuma gasar wasa kwakwalwa za ta sami ci gaba a kasar Sin. Mun ga kasar Sin ta ci nasarar shirya gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu. A bayyane ne kasar Sin ta yi iyakacin kokari a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma a bayyane ne kasar Sin ta yi matukar kokari a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, a sa'i daya kuma, kasar Sin ita ma tana yin namijin kokari a gun wannan zama na gasar wasa kwakwalwa ta duniya. Ko shakka babu, gasar wasa kwakwalwa ta duniya da ake yi yanzu a Beijing ita ce gaggarumin biki ga kasar Sin."

Koda yake gasar nan wato gasar wasa kwakwalwa ta duniya ba ta da sikeli mai girma kuma ba ta iya kawo babban tasiri ga duk duniya ba idan an kwatanta ta da gasar wasannin Olympic da kuma gasar wasannin Olympic ta nakasassu, amma gasar nan tana da ma'anar musamman, dalilin da ya sa aka fadi haka shi ne domin a karo na farko an hada ire-iren wasa kwakwalwa wadanda suka fi samun karbuwa daga wajen jama'ar duk duniya tare a gun gasar, kuma an sa masu wasa kwakwalwa da su shiga dandalin babbar gasar duniya, haka ya sa 'yan wasa kwakwalwa iri daban daban su shiga wani sabon mataki. Mun hakkake cewa, a cikin 'yan shekaru masu zuwa, kuma a karkashin kokarin da fannoni daban daban da abin ya shafa suke yi tare, gasar wasa kwakwalwa za ta kara jawo hankulan jama'ar kasashen duniya kamar yadda gasar wasannin Olympic take. (Jamila Zhou)


1 2