Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-15 09:22:41    
An yi zama na farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya a Beijing

cri

Kamar yadda kuka sani, a watan Agusta na bana, an yi zama na 29 na gasar wasannin Olympic a birnin Beijing na kasar Sin, kuma an gama lafiya, daga baya kuma a watan Satumba na bana, an yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu a Beijing, ana iya cewa, an sami babbar nasara sau biyu. Yanzu dai ana shirya zama na farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya a kasar Sin.

A ran 3 ga wata, a nan birnin Beijing, an fara zaman farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya, wannan shi ne gasar wasanni ta matsayin duniya daban da kasar Sin ta shirya bayan da ta kammala gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu a Beijing. 'Yan wasa kusan dubu 3 sun halarci gasar, to, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani kan wannan.

Kawancen wasa kwakwalwa na duniya ne ya shirya zaman farko na gasar wasa kwakwalwa ta duniya, kamar yadda kuka sani, an kafa kawancen ne a shekarar 2005, makasudin kafuwarsa shi ne domin ingiza bunkasuwar wasannin chess da na karta a duk duniya. Daga baya kuma, kawancen wasa kwakwalwa na duniya ya yi shawarwari da kwamitin wasannin Olympic na duniya kan batun da abin ya shafa, a karshe dai, sun tsai da cewa, za su zabi birnin da ya shirya gasar wasannin Olympic da ya shirya gasar wasa kwakwalwa ta duniya a lokaci mai dacewa wato bayan da aka gama gasar wasannin Olympic ta yanayin zafi ko na sanyi, shi ya sa Beijing ya zama birni na farko da ya shirya gasar wasa kwakwalwa ta duniya. Shugaban kawancen wasa kwakwalwa na duniya Jose Damiani ya yi mana bayani cewa,  "Kawancenmu ya nuna babbar godiya ga kwamitin shirya gasar na kasar Sin saboda namijin kokarin da ya yi domin shirya wannan gasar wasa kwakwalwa. A gun gasar, gaba daya 'yan wasa wajen dubu 3 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi sama da 140 sun shiga gasar, wasannin gasa suna kumshe da wasanni iri biyar wato wasan karta da wasan darar chess na duniya da wasan darar chess na kasar Sin da sauransu."

Za a shafe kwanaki 16 ana yin gasar, wato an fara gasar daga ran 3 ga wata kuma za a kawo karshenta a ran 18 ga wata. Kuma 'yan wasa za su yi takara domin neman samun lambobin zinariya 35. A karkashin goyon bayan hadaddun kungiyoyin wasannin biyar, wato wasan karta da wasan darar chess na duniya da wasan darar chess na kasar Sin da sauran wasannin chess biyu, gasar wasa kwakwalwa ta duniya ta riga ta kai matsayin koli a duniya ko da yake wannan a karo na farko ne da aka shirya irin wannna gasa. Kuma kusan dukkan fitattun 'yan wasa a duk duniya sun zo Beijing domin shiga gasa. Alal misali, shaharariyar 'yar wasan darar chess na duniya daga kasar Rasha wadda ake kiranta da suna 'sarauniyar wasan darar chess ta duniya' Alexandra Kosteniuk da 'dan wasan darar chess daga kasar Sin wanda ya taba zama zakaran duniya Guli da 'dan wasan karta daga kasar Amurka wanda shi ne zakaran duniya Bob Hamman da sauran shahararrun 'yan wasa sun halarci gasar tare, lallai ana iya cewa, gasar nan ita ce gaggarumin bikin cudanyar basirar dan adam.


1 2