Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-13 16:22:43    
Madam Lu Wanxiang, shugabar gari kuma 'yar kabilar Miao ta gundumar Leishan ta lardin Guizou na kasar Sin

cri

Madam Lu Wanxiang ta ba da gudummawa daga fannoni da yawa domin kara samun kwanciyar hankali da zaman jin dadi ga jama'a 'yan kabilar Miao. Kauyukan da ke garin Langde a warware suke, kuma da akwai babban nisa a tsakaninsu, shi ya sa madam Lu takan shafe lokaci mai tsawo tana tafiya a kan hanyoyin tuddai domin zuwa gidajen mutane.

Gajiyar da ta samu a jikinta ba wani abu ba ne, abun da ya bata mata zuciya shi ne, wani sa'i wasu kauyawa ba su fahinci kyakkyawan nufinta ba. Alal misali, wajen aikin ba da ilmi, ko da yake gwamnatin kasar take gudanar da aikin samun ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9, amma da akwai yara na wasu kauyuka wadanda kullum wasa suke so, ba su son zuwa makaranta, iyayensu ma sun yi kunnen uwar shege a gaban halin da suke ciki. Domin shigar da yaran makaranta, kusan an ce madam Lu Wanxiang ta je wajen iyayensu domin zantawa da su a kowace rana, ta yi ayyuka da yawa. Sakamakon haka yanzu dukkan 'yan makarantar firamare sun shiga cikin makaranta, amma har ila yau da akwai wasu 'yan kamaratar sakandare wadanda suka daina karatu suna gida. Madam Lu ta ce,

"Akwai wasu 'yan makarantar sakandare wadanda halayen tattalin arzikin gidajensu ke da kyau, amma ba su son karatu, kuma iyayensu ba su nuna goyon baya ga aikinmu, wato sun kifta idon yaran da su daina zuwa makaranta. Wani sa'i na je gidajensu don komar da yaransu makaranta, amma sun ki amincewa da ni, sabo da haka na yi bakin ciki sosai a wancan lokaci."

Ko da yake madam Lu Wanxiang ta sha wahaloli da yawa wajen aikinta, amma ya gwammace yanzu tana jin muryar zargin da fararen hula suke yi mata, ba ta son jin muryar kukan su a nan gaba, ta amince cewa, wahalolin da take sha yanzu na dan lokaci ne, sabo da haka ba ta taba zubar da hawayenta sabo da wahalolin da ta sha wajen aikinta ba.


1 2