Yankin kabilar Miao da ta Dong mai ikon tafiyar da harkokin kansa yana kudu maso gabashin lardin Guizhou da ke kudu maso kudancin kasar Sin, a can da akwai tuddai masu launin tsanwa shur da koguna masu ruwa garai-garai, mutanen da ke zama a wannan yanki suna da kirki da sahihanci, yawancinsu 'yan kabilar Miao ne kuma tare da sauran kananan kabilu, a can kuma da akwai wata mataimakiyar shugabar gari 'yar kabilar Miao wadda take da shekaru 30 da haihuwa, sunanta kuwa shi ne Lu Wanxiang.
'Yan kabilar Miao maza da mata dukkansu sun kware wajen yin rawa da waka, kuma suna cike da kwazo da himma, madam Lu Wanxiang, 'yar kabilar Miao kuma shugabar garin Langde ita ma ba a cire mata hula ba. A shekarar 2002, madam Lu ta gama koyo daga kolejin kabilu na Guizhou, sabo da tana son waka da rawa, kuma kullum tana cikin annashuwa da farin ciki, shi ya sa ko kusa ba ta yi tsammani ta kama gurbin aikinta na kula da harkokin hukuma bayan ta gama karatu daga jami'a ba. Bayan da ta ci zaben zaman mataimakiyar shugabar gari a shekarar 2006, ta sa kafa a dukkan kauyuka 41 manya ko kanana na garin Langde. Ta ce,
"A kauyenmu akan gamuwa da matsalar kiyaye zaman lafiya, musamman ma matsalar kwana-kwana, ya kamata ma'aikatan hukuma su je sassa daban-daban a lokaci-lokaci don duba hanyoyin samar da wutar lantarki, da daidaita sauran matsalolin jama'a, wato daidaita sabanin da ke tsakanin fararen hula. A lokacin damina akan yi ruwan sama da yawa, har duwatsu sun zagwanye a wasu wurare, amma duk da haka, mukan je kauyuka daban-daban don duba aiki."
Fifitattun nasarorin da madam Lu Wanxiang ta samu wajen aikinta sun samu amincewa daga magabatanta, Mr. Jiang Dajun, mataimakin shugaban gundumar Leishan ya yi mata yabo sabo da ayyuka masu kyau da take yi wajen kwana-kwana, ya ce,
"Takan yi aiki cikin nitsuwa, kowanen aikin da muka danka mata ta yi tsare-tsare da kyau, kuma ta kammala aiki bisa bukatar da muka yi mata cikin lokaci. Ita wata ma'aikaciyar hukuma ce bisa matsayin gunduma, kuma kwararriya ce wajen aiki. Mun gamsu da dukkan ayyukan da ta yi sosai".
1 2
|