Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-08 18:29:20    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ce, yaki da bala'un girgizar kasa da ayyukan ceto sun bayyana halayya mai kyau ta al'ummar kasar Sin

cri

'Dan birnin Chengdu mai shekaru 36 da haihuwa Mr. Chen Yan ya zama wani mutumin da ya yi aikin sa kai da kansa a yankunan da girgirzar kasa ta shafa. Mr. Chen ya ce,

'Wasu mutane sun tambaye ni cewa, me ya sa ka yi aikin sa kai ? Me ya sa ka ceci rayuka na sauran mutane ba tare da yin la'akari kan rayuwarka ba ? Amsata ita ce, sabo da na zama 'dan lardin Sichuan ne, ni Basine ne. A lokacin kuma, ina son cewa, sabo da ina da rai har lokacin. Kasar Sin mahaifarmu ce, a lokacin da mahaifiya take cikin mawuyacin hali, babu dalilin da ba za mu dauki matakai ba. Idan ina da rai, zan ba da duk karfina ga kasar Sin mahaifata.'

Mr. Hu Jintao ya ci gaba da cewa,

'A yayin da muke yaki da babbar girgizar kasa, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, da sojojinmu, da jama'armu mun hada kanmu da zuciya daya, mun kafa wata babbar ganuwa a gaban bala'un girgizar kasa, wannan kuma ya bayyana halayya mai kyau ta al'ummar kasar Sin wato mun hada kanmu wajen daidaita matsala, mun gama gwiwa sosai mun yi kokari tare.'(Danladi)


1 2