A ran 8 ga wata da safe a zauren babban dakin taro na jama'ar kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta kira taron ba da kyautar yabo ga mutanen da suka fi ba da taimako wajen yaki da bala'un girgizar kasa da ayyukan ceto. Shugabannin kasar Sin da na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da dai sauransu sun halarci taron.
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin yayi jawabin cewa, babbar girgizar kasa da karfinta ya kai awo 8 bisa ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ta fi kawo hasara da wuyar gudanar da ayyukan ceto tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, wannan girgizar kasa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan budu 70, a yayin da aka yi hasarar tattalin arziki da yawansa ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 840. Mr. Hu Jintao ya ce,
'Bala'un girgizar kasa sun ba mu umurni, don lokaci yana da muhimmanci wajen ceton rayuka. A wannan karo, mun gudanar da ayyukan ceto da suka fi sauri kuma suka fi shafar bangarori daban daban a tarihi, mun rubanya kokari wajen ceton rayukan jama'a, da kuma rage hasarar daga wannan girgizar kasa.'
1 2
|