Bisa shirin zayyana da aka tsara, an ce, an shimfida kewayayyiyar hanyar tsere mai tsawon mita 400 kuma mai launin zinariya a cibiyar filin wasan. A karkashin sararin sama mai launin shudi, wannan hanyar tsere da koren bishiyoyin da suke girma sosai a kewayen filin wasa suna kara wa juna haske, sai ka ce, wani babban dragon ma launin zinariya yana hutu a tsakanin bishiyoyi, yana jiran 'yan wasa. A kan hanyar tsere, akwai gangara da yawa, wadanda tsayinsu ke sha bamban da juna, tsayin mafi tsayi ya kai misalin mita 4. Su ne abubuwan tsoshewa da aka samar wa 'yan wasa, haka kuma, su ne abubuwan da 'yan wasa suka yi amfani da su domin nuna ingantacciyar fasaharsu. A lokacin gasar, 'yan wasa sun iya tsalle-tsalle da tafiya, sun kuma iya yin motsi iri daban daban tare da kekunansu masu hananan hayoyi a kan wannan hanyar tsere mai launin zinariya.
Hadaddiyar kungiyar wasan tseren keke ta kasa da kasa ta fito da tabbatacciyar ka'ida kan kasar da aka yi amfani da ita domin samar da wadannan gangara. Kamata ya yi a tabbatar da ganin yawan rairayin da ke cikin wadannan abubuwan toshewa ya kai kashi 20 cikin kashi dari, sa'an nan kuma, kada a hada rairayi da kasa tare kai tsaye, ta yadda 'yan wasa za su ji dadi a lokacin gasar. Mai gina filin wasan sun sha yin dabara wajen samun kasar da ta biya bukata. A farkon wannan shekara, an kafa kungiyar musamman domin neman kasa. Bayan wata guda ko fiye, wannan kungiya ta sami kasa iri-iri guda 6 daga wurare daban daban na Beijing, ta kuma zabi wasu 3 daga cikinsu, ta aika da su zuwa hadaddiyar kungiyar wasan tseren keke ta duniya cikin kwalaba. Amma kwararru na hadaddiyar kungiyar wasan tseren keke ta duniya sun yi shirin zuwa Beijing domin zaben kasar da ta fi dacewa da kansu. In ba a tabbatar da kasar da za a yi amfani da ita ba, to, za a dakatar da gina wannan filin wasa. Amma abin farin ciki shi ne bayan da wadannan kwararru suka sha yin gwaje-gwaje da kuma kwatantawa a Beijing, a karshe dai, sun tabbatar da kasar da suke so. Bayan da aka hada wani abun musamman a cikinta, ko ana ruwan sama, irin wannan kasa ta iya karbar ruwa sosai, 'yan wasa ba za su gamu da tabo da yawa a kan hanyar tsere ba, za a yi gasa bisa shirin da aka tsara a da. 1 2
|