Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-23 15:18:01    
Filin tseren keke mai kananan hayoyi na Laoshan

cri

In an tabo magana kan tseren keke mai kananan hayoyi wato BMX a Turance, mene ne ku kan tuna da su, nagartacciyar fasaha ta musamman wajen hawan keke? Ko kuma ganin keke mai kananan hayoyi yana tsalle-tsalle a sararin sama? Ko kuma ra'ayin da 'yan wasan suke nunawa, wato ba su ji tsoron shan kaye ba, kuma suna son kalubalanci iyakar kwarewarsu? Irin wannan wasa mai matukar ban sha'awa da ya bullo a kasar Amurka yana bazuwa a kasar Sin a shekarun nan da suka wuce. A wurare da yawa na birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda kuma za a yi gasar wasannin Olympic a shekara mai zuwa, dimbin matasa suna wasa da irin wadannan kekuna na musamman, kekunan kuwa suna tafiya a tsakanin matakai masu tsayi daban daban.

A shekarar 2008, a karo na farko ne tseren keke mai kananan hayoyi zai bullo a cikin gasar wasannin Olympic. Za a yi wannan shiri a filin tseren keke mai kananan hayoyi na Laoshan da ke yammacin Beijing, yana kuma makwabtaka da dakin tseren keke na Laoshan da kuma dakin tseren keke a tsakanin tsaunuka na Laoshan. Fadinsa ya ba ya kai kadada 2. A matsayinsa na dakin wasa na wucin gadi, filin tseren keke mai kananan hayoyi 2 zai karbi 'yan kallo dubu 4 a lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta Beijing.


1 2