Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-23 15:16:16    
Filin wasan Triathlon na gasar wasannin Olympic

cri

Fadin hanyoyin tsere ya yi kusan daidai da na filayen wasan kwallon kafa guda 2. A karo na farko ne aka shimfida hanyoyin tsere masu fadin haka a kasar Sin. An shimfida hanyoyin tsere masu inganci da aka sarrafa su a masana'antu tare. Wadannan hanyoyin tsere da aka yanka su yadda ya kamata sun rufe cikakken filin wasan, ta haka, dukkan doron kasa na filin wasan ya yi laushi sosai. Sa'an nan kuma, an cika giyabun da ke tsakanin hanyoyin tseren yadda ya kamata, har ma mutane ba su gane cewa akwai giyabu ba. Wasu 'yan wasa na gida da na ketare da suka yi gasar share fage a wajen sun nuna matukar gamsuwa kan muhallin halittu a wannan filin wasa da kuma ingancin hanyoyin tsere.

Ran 15 zuwa ran 16 ga watan Satumba na shekara ta 2007, an kira gasar cin kofin duniya ta wasan Triathlon ta 'Good Luck Beijing' a filin wasa da ke matarin ruwa na Shisanling. Wannan ne gasar share fage da aka yi domin shirin wasan Triathlon na gasar wasannin Olympic ta Beijing. Masu shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sun kara yawan kujeru, ta haka, yawan 'yan kallo sun karu zuwa dubu 6 a maimakon dubu daya a da. Ban da wannan kuma, an tsawaita tsawon hanyar ninkaya da ke gaban madatsar ruwan, ta haka, tsawon hanyar ninkaya ya yi daidai da na shirin wasan Triathlon na gasar wasannin Olympic. Bugu da kari kuma, don tabbatar da jin dadin kallon gasar, an shimfida wata sabuwar hanya mai tsawon mita 700 bisa hanyar rarraba ambaliyar ruwa ta matarin ruwa na Shisanling, ta haka, za a iya biyan bukatun 'yan wasa da za su iya wucewa dandamalin 'yan kallo har sau 6 a cikin gasar, 'yan kallo za su iya jin dadin kallon gasar.


1 2