Wasan Triathlon, wani irin wasa ne da ya kunshi ninkaya da tseren keke da kuma gudun fanfalake, ya kuma kawo wa 'yan wasa kalubale ta fuskar karfi da sauri da fasaha a lokaci daya. Ya bullo ne a shekarar 1973. A shekara mai zuwa, irin wannan wasa da ya kalubalanci iyakar kwarewar mutane zai sauko matarin ruwa na Shisanling da ke nan Beijing saboda za a yi gasar wasannin Olympic a lokacin.
Shahararren matarin ruwa na Shisanling na cikin gundumar Changping da ke arewacin Beijing, nisan da ke tsakaninsa da yankin tsakiya na Beijing ya kai misalin kilomita 40. A shekarar 2008, a lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasan Triathlon da suka fito daga wurare daban daban na duniya za su kara da juna a cikin gasar ninkaya mai tsawon kilomita 1.5 da tseren keke mai tsawon kilomita 40 da kuma gudun fanfalake mai tsawon kilomita 10 a wannan shahararren matarin ruwa. Yanzu a lokacin da kuke yawo a kan madatsar ruwan, ku yi hange nesa, to, za ku iya ganin cewa, shuddan hanyoyin tsere da shudin sararin sama suna kara wa juna haske, suna da kyaun gani sosai tare kuma da ni'imtaccen matarin ruwa na Shisanling.
1 2
|