Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-18 18:21:10    
Kasar Sin ta yi ta kyautata matsayinta na bai wa kasashen waje taimako

cri

Bugu da kari kuma, gwamnatin Sin ta dade tana mai da hankali kan horar da kwararru na kasashen waje don ba da taimako ga wadannan kasashe da su iya kyautata karfinsu na raya su da kansu. Ya zuwa yanzu dai, jami'ai da kwararru masu fasaha kusan dubu 100 sun zo kasar Sin domin shiga kos-kos da ayyukan horaswa. Musamman ma a shekarun baya, kasar Sin ta sha shirya kos-kos da ayyukan horaswa da tarurukan kara wa juna sani domin kasashen Afirka, inda kasashen Afirka suka iya morewa da kuma koyon fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin bunkasuwa. Fan Xiaojian, darektan ofishin jagorancin ba da taimako ga matalauta da kuma ayyukan bunkasuwa da ke karkashin shugabancin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ba da taimako wajen kawar da talauci a Afirka daga fannoni da yawa. Mr. Fan ya ce,"Kasar Sin tana son ta more fasahohin da ta samu daga wajen kawar da talauci da raya zaman al'ummar kasa tare da kasashen Afirka, za ta kuma ci gaba da ba da taimako a fannonin kyautata albarkatun kwadago da ba da fasahohin da abin ya shafa."

Mr. Wang Shichun ya kuma yi karin bayani da cewa, ba da taimako ga kasashen waje ya iya sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin wadannan kasashe, haka kuma, ya iya inganta dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa. Ya kuma fayyace cewa,"Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta ci gaba da gama kanta da hukumomin da abin ya shafa wajen gaggauta ba da taimako, ta haka, jama'ar kasashen da suka samu taimako za su samu alheri. Bayan wannan kuma, kasar Sin za ta yi ta kyautata manufofi da dokoki da ke shafar ba da taimako ga kasashen waje, za ta kuma kyautata matsayinta na kulawa da ayyukan ba da taimako da sakamakon da aka samu daga wajen ba da taimako. Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta ci gaba da yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen waje, za ta koyi tunani da matakan da kasashen duniya suka dauka wajen ba da taimako ga kasashen waje, za ta yi ta kyutata matsayinta na ba da taimako ga kasashen waje."(Tasallah)


1 2