Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-18 18:21:10    
Kasar Sin ta yi ta kyautata matsayinta na bai wa kasashen waje taimako

cri

Don taimakawa kasashe masu tasowa a fannin raya tattalin arzikinsu, kasar Sin ta dade tana himmantuwa wajen ba su taimako ta fuskar tattalin arziki da kiwon lafiya, ta kuma sami sakamako mai kyau. Jami'an kasar Sin sun bayyana cewa, ko da yake kasar Sin ta sami sakamako a fannoni da dama, amma kasar Sin tana bukatar daidaita batutuwa da yawa wajen gudanar da ayyukan ba da taimako ga kasashen waje, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da bai wa kasashe masu tasowa tallafi, za ta kuma yi ta kyautata matsayinta a wannan fanni.

Wang Shichun, shugaban sashen bai wa kasashen waje taimako na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa,"Gwamnatin Sin tana ba da taimako, sa'an nan kuma, don raunana nauyin da aka danka musu a harkokin tattalin arziki, kasar Sin tana yafe wa wasu kasashe masu fama da taluaci da suka ci basusuka da yawa, suka kulla dangantakar zumunci a tsakaninsu da kasar Sin da kuma kasashe mafiya fama da rashin ci gaba basusukan da suka ci daga wajen kasar Sin ba tare da sharadi ba. Haka kuma, kasar Sin ta karfafa gwiwa da kuma mara wa masana'antun kasar Sin da suke da karfi da kuma kyakkyawan suna baya da su zuba jari da kuma yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa. Irin wannan hadin gwiwa yana da amfani wajen kara samar da guraban aikin yi da kuma samun karin kudin haraji a wurin, haka kuma, yana ba da taimako wajen sa kaimi kan bunkasuwar bangarorin 2 duka"

An yi karin bayani da cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, kasar Sin ta yafe wa kasashe 49 na Afirka da Asiya da yankin Caribbean da kudancin tekun Pacific basusukan da suka ci har sau 374. Bisa bukatun da wasu kasashe masu tasowa suke bayarwa, kasar Sin ta yi ta tura kungiyoyin kiwon lafiya zuwa wadannan kasashe. Tun daga shekarar 1963 har zuwa yanzu, kasar Sin ta aika da ma'aikatan kiwon lafiya kimanin dubu 20 zuwa kasashe da yankuna 65 na Asiya da Afirka da Latin Amurka da gabashin Turai.

1 2