Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 21:42:12    
Dakin cin abinci mai suna darare 1001 da ke samar da abinci irin na Larabawa mai dadin ci

cri

Babu tamtama makasudi mafi muhimmanci na zuwa dakin cin abinci na darare dubu 1 da 1 shi ne dandano abinci mai dadin ci irin na Larabawa. Malam Hassan ya yi mana karin bayani kan wasu abinci da suka fi jawo sha'awar masu cin abinci.

"Masu cin abinci su kan yi odar gasassun abinci irin na Larabawa da kuma wani irin abinci mai dadin ci na Larabawa daban wato Couscous. Sinawa da yawa su kan je dakin cin abincinmu, su yi odar wannan abinci bayan da suka ga karin bayani da aka yi wa Couscous a talibijin, suna son su gano mene ne Couscous."

Larabawa sun fi nuna gwaninta wajen gasa abinci, suna kuma fi son irin wannan abinci, sa'an nan kuma, gasasshen abinci ya fi nuna halin musamman na al'adar abinci irin na Larabawa.

A cikin dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, madam Wang Lijuan tana cin abinci tare da abokan aikinta, sun yi odar wani shahararren abinci a wannan dakin cin abinci wato gasasshen dan tunkiya. Madam Wang ta taba yin shekaru da dama tana yin karatu a Sham, ta san abinci irin na Larabawa sosai. Ta yi mana karin bayani da cewa, kuku-kuku su kan zabi 'yan tunkiya a yayin da suka samar da gasasshen dan tunkiya. Bayan da suka yanka wani dan tunkiya bisa al'adun musulmai, sun ajiye wannan dan tunkiya a cikin ruwan da ke cike da kayayyakin kamshi irin na Larabawa iri-iri gomai, daga baya, sun gasa wannan dan tunkiya a cikin obin. Da zarar naman dan tunkiya ya kusan gasuwa, kuku-kukun sun fitar da shi a waje da obin, su sa shinkafa irin ta kasar Thailand da wake da kuma kwayoyin itatuwan pine a cikin dan tunkiyar, daga baya sun sake ajiye shi cikin obin.

"Da wuya ne sosai a fito da irin wannan abinci. Wasu lokuta, naman tunkiya bai yi ba, wasu lokuta kuma, an gasa shi fiye da kima, har ma naman dan tunkiyar ya kone. Ga gasasshen dan tunkiya a kan teburinmu, fatarsa tana garas-garas, yana da dadin ci da kamshi, kuma launin fatarsa ya yi kyau sosai. Ban da wannan kuma, akwai shinkafa da kayan lambu. Wannan gasasshen dan tunkiya ya ishe mu daidai, yana da dadin ci amma ba tare da biyan kudade da yawa ba."

A cikin labaru da yawa da aka rubuta kan al'adun gargajiya da ke yaduwa a kasashen Larabawa a arewacin Afirka, a kan ambaci abinci mai suna Couscous, amma mene ne Couscous? Masu sauraro, in kun zo dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, to, za ku san mene ne wannan Couscous.

A cikin dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, a kan samar da gurasa da nama da kayan lambu, shi ne shahararren Couscous.

Saboda madam Wang ta sha zuwa wannan dakin cin abinci, shi ya sa ta gaya mana cewa, idan abokanta daya ko biyu da ita sun zo nan, to, ta kan yi odar wannan Couscous. Madam Wang ta ce,"Babu bambanci a tsakanin Couscous da na ci a nan da kuma wanda na taba ci a Sham. Na fi son ci naman tunkiya. Tilas ne a hada gurasa da miya, ta haka tana da dadin ci sosai. In kun dafa Couscous a gida, za ku iya zaben kayan lambu da kuke so."

Ban da abinci mai sigar musamman ta al'adar Larabawa da muka ambata a baya, akwai abinci irin na Salad da kuma kayan shaye-shaye da kuma abin sha masu halin musamman na Larabawa.

Bayan budewarsa yau da shekaru 10 da suka wuce, dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1 yana ta jawo hankulan Sinawa masu yawa da su ci abinci a ciki saboda tsantsar abinci irin na Larabawa da kuma halin musamman na al'adar Larabawa. Sa'an nan kuma, dimbin mutanen da suke zama a nan Beijing daga kasashen waje suna son cin abinci a wannan dakin cin abinci saboda ya yi suna sosai a tsakanin mutanen da suka zo daga kasashen waje. Ga shi, Mr. Thomas da ya zo nan Beijing aiki daga kasar Jamus, ko da yake ya yi rabin shekara ko fiye kawai yana nan Beijing, amma ya riga ya ci abinci a wannan dakin cin abinci har sau 3.

"Wannan shi ne karo na 3 da na ci abinci a nan. Wurin da nake ciki yana dab da wannan dakin ci abinci, yana kwana a wannan titi, shi ya sa na iya zuwa nan cikin sauki. Abincin da ake samarwa a nan na da dadin ci sosai, kuma ana bayar da hidimomi masu inganci. Na iya dandana abinci iri daban daban a nan, shi ya sa yau na sake zuwa nan kuma tare da iyalina."

Masu sauraro, ko kun zo daga kasashen Larabawa, yanzu kuna begen abincinku, ko kuma kun zo daga sauran kasashe, kuna son dandana abinci mai dadin ci irin na Larabawa, in kun zo dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, to, tabbas ne za ku cika burinku.


1 2