In an tabo magana kan wani shahararren littafi na Larabawa na gargajiya mai suna darare dubu 1 da 1, to, tabbas ne ba za ku yi mamaki a kansa ba, tatsuniyoyi da almara da labaru masu ban mamaki da kuma kayatarwa da ke cikin wannan littafi sun sanya mutane su nuna sha'awa sosai kan wannan yanki mai ban mamaki. A nan Beijing, akwai wani dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, inda ake iya dandana abinci irin na Larabawa gaba daya.
Dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1 yana gundumar Chaoyang da ke gabashin birnin Beijing. Yana dab da titin Sanlitun mai yawan gidajen nishadi da kuma yankin da aka fi samun yawan ofisoshin jadakanci na kasashen waje a kasar Sin. Tsawon kafuwarta ya kai shekaru 10. Shi ne dakin cin abinci na farko da ake samar da abinci irin na Larabawa gaba daya a nan Beijing. Dalilin da ya sa ake samar da abinci irin na Larabawa gaba daya shi ne domin mai dakin cin abincin wani dan kasar Sham ne, haka kuma, kuku-kukun da ke aiki a nan wannan mai dakin cin abincin ne ya gayyace su daga kasashen Larabawa. Malam Hassan, wanda ya zo daga Sham, yana aiki a wannan dakin cin abinci a matsayin wani kuku. Ya gaya mana cewa"A shekarar 1998, na zo kasar Sin tare da mai dakin cin abincinmu. A yayin da muka bude kofar dakin cin abincinmu, mun gayyaci wasu jakadun kasashen Larabawa a kasar Sin da kuma sauran jakadun kasashen waje domin shirya wani liyafa. Mun sami babbar nasara a wancan lokaci. Dakin cin abincinmu ya zama na farko da yake samar da abinci irin na Larabawa gaba daya a kasar Sin."
Masu sauraro, da zarar ku shiga dakin cin abinci mai suna darare dubu 1 da 1, sai kun gano al'adar Larabawa yana cika duk dakin cin abincin, a ko ina kun iya gano abubuwan da ke shafar al'adar Larabawa.
Malam Hassan ya yi karin bayani da cewa, an kayatar da wannan dakin cin abinci a daidai bisa salon gine-gine na gargajiya na Larabawa. Dalilin da ya sa aka fito da irin wannan muhalli mai sigar musamman ta al'adar Larabawa shi ne domin neman sanya masu cin abinci su ji kamar yadda suke cin abinci a cikin wani dakin cin abinci da ke wani birnin Larabawa.
"Masu cin abinci suna son cin abinci tare da more idanunsu da raye-raye irin na Larabawa. Suna son irin wannan halin musamman na al'adar Larabawa da ke sha bamban da nasu, suna jin dadin cin abinci mai dadin ci da kuma kallon raye-raye ba tare da sauraren kara ba, muna samar musu hali mai kyau wajen cin abinci da kuma yin hira tare."
1 2
|