Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 15:11:50    
Jam'iyyun Zimbabwe sun cimma yarjejeniyar raba madafun iko

cri

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce, a cikin gwamnatin gamin gambiza da aka kafa bisa yarjejeniyar raba madafun iko, jam'iyyar da ke rike da ragamar mulki da kuma jam'iyyar adawa sun raba iko cikin daidaito, amma kila za su yi wa juna tarnaki a ayyukan da za a gudanar a nan gaba, har ma zai kawo illa ga gwamnati a wajen tafiyar da harkokin mulki. Sa'an nan, a yayin da Mugabe da Tsvangirai suke raba iko a kan sojoji da 'yan sanda, idan an sake samun rikici a tsakanin jam'iyyun biyu, za a kara samun tsanantar lamura.

A game da haka, shugaba Mugabe ya bayyana cewa, shi da kuma jam'iyyarsa ta ZANU-PF za su bi yarjejeniyar da aka cimma, su hada gwiwa da jam'iyyar MDC da ke karkashin jagorancin Tsvangirai, su bauta wa sabuwar gwamnatin gamin gambiza da aka kafa. Ya kuma yi kira ga jam'iyyun biyu su kawar da sabaninsu, su nuna wa al'umma cewa, gwamnatin gamin gambiza na iya tafiya yadda ya kamata.

A nasa bangaren, a matsayinsa na firaministan kasar, Mr.Morgan Tsvangirai ya yi kira ga jam'iyyun biyu da su kawo karshen kiyayyar da ke tsakaninsu, su hada kansu. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su janye takunkumi a kan Zimbabwe, kuma Zimbabwe za ta bude kofarta ga gudummowar kasa da kasa.(Lubabatu)


1 2