Jiya 15 ga wata, shugabannin jam'iyyun kasar Zimbabuwe sun yi bikin rattaba hannu a kan yarjejeniyar raba madafun iko, kuma sun sanar da kafuwar gwamnatin gamin gambiza. Wannan kuma ya nuna cewa, rikicin siyasa da ya faru a kasar a sanadin babban zaben da aka gudanar a watan Maris da ya wuce ya kusan kawo karshensa, kuma Zimbabwe ta shiga wani sabon zamani da jam'iyyu biyu ke rike ragamar mulkinta cikin hadin gwiwa.
Bisa yarjejeniyar raba madafun iko, sabuwar gwamnatin gamin gambiza na kunshe da jam'iyyu biyu, wato jam'iyyar ZANU-PF da ta MDC, kuma suna raba ikon gwamnati cikin daidaito. Mr.Robert Mugabe zai ci gaba da rike mukamin shugaban kasar da kuma ikon sojoji na kasar, a yayin da Morgan Tsvangirai zai zama firaministan kasar, wanda zai shugabanci majalisar gudanarwa da ke kunshe da ministocinsa, da kuma jagoranci hukumomin tsaro na kasar, ciki har da hukumar 'yan sanda da kuma na 'yan leken asiri. Nan gaba, zai kuma kula da harkokin tattalin arziki da zaman al'umma na kasar.
Mr.Thabo Mbeki, shugaban kasar Afirka ta kudu kuma shugaban kungiyar SADC ta raya kudancin Afirka, wanda kuma ya kasance mai shiga tsakani kan matsalar Zimbabwe, tare kuma da Jakaya Kikwete, shugaban kungiyar tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Tanzania, da dai sauran shugabannin kasashen kudancin Afirka da dama sun halarci bikin.
A gun bikin, Mr.Thabo Mbeki ya yi jawabin cewa, cimma yarjejeniyar da kuma kafa gwamnatin gamin gambiza ba wai ke nan aka kawo karshen matsaloli ba, a'a, matakin da ya kamata a dauka a gaba shi ne jam'iyyun biyu su gaggauta hadin gwiwa a tsakaninsu. Mr.Jakaya Kikwete shi ma cewa ya yi, ko da yake an rattaba hannu a kan yarjejeniyar raba madafun iko, amma Zimbabuwe na cigaba da fuskantar matsaloli. Duk da haka, sun kuma bayyana farin cikinsu dangane da cimma yarjejeniyar da aka yi, sun ce, abin farin ciki ne jam'iyyun Zimbabwe sun cimma yarjejeniyar, wadda kuma ta sake shaida cewa, kamata ya yi 'yan Afirka su daidaita batutuwan Afirka da kansu, kuma ta samar da misali wajen daidaita gardamomi irinsa a nan gaba.
Masharhanta sun yi nuni da cewa, cimma yarjejeniyar raba madafun iko da jam'iyyar ZANU-PF da ta MDC suka yi ya zama mafari ne kawai a wajen daidaita matsalolin siyasa da tattalin arziki na Zimbabwe, tilas ne jam'iyyun biyu su hada gwiwa su daidaita dimbin matsalolin Zimbabwe ta fuskokin siyasa da tattalin arziki da diplomasiyya da zaman al'umma da dai sauransu.
1 2
|