Bugu da kari kuma, an yaba wa na'urori marasa shinge a filaye da dakunan wasanni da kauyen Olymics na nakasassu. Shugaban tawagar wasannin Olympics na nakasassu ta kasar Bulgaria, Mr.Iiia Lalov, wanda ya kawo ziyara a nan birnin Beijing a karo na uku, yana ganin cewa, na'urori da hidima da aka bayar a kauyen Olympics na nakasassu suna da kayatarwa. Ya ce,
'Babban mataki na na'urorin wasanni na gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ya fi burge ni. Kasar Sin ta bayar da fiyale da dakunan wasanni da wuraren kwana masu kyau ga 'yan wasa nakasassu. A ganina, ban taba ganin irin wannan kauyen Olympics na nakasassu, da ayyukan tsara gasanni masu kyau ba.'
Shugaban tawagar wasannin Olympics na nakasassu ta kasar Sri Lanka Mr. Rajive Wickramashinghe ya fi mai da hankali kan abinci da ruwan sha a kasar Sin. Ya gaya mana cewa,
'A nan birnin Beijing, na ci abincin kasar Sin na hakika, abincin kasar Sin yana da dadin ci kwarai da gaske. Jama'ar kasar Sin suna da hikima sosai, ban san yadda suke dafa abinci mai dadin ci kamar haka ba.'(Danladi) 1 2
|