A ran 12 ga wata, an riga an gama wasu gasanni, har ma an riga an kawo karshen rabin shirin dukkan gasanni na wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. 'Yan wasa da malamai da ke horar da 'yan wasa, sun yaba wa ayyukan shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing sosai da sosai.
Shahararren 'dan wasa na gasar harbi da kibiya na kasar Korea ta kudu Mr. Lee Hong Goo ya gaya wa wakilinmu cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta burge shi sosai. Ya ce,
'Wannan gasa tana da kyau. Na taba shiga gasannin Olympics na nakasassu a shekarar 2000 da ta 2004, amma a ganina, gasar da aka shirya a Beijing ta fi kyau, musamman ma kasar Sin tana kulawa da mu 'yan wasa sosai kan bus, wanda ya ba mu sauki sosai wajen tashi da sauka. Fiyale da dakunan wasanni suna kusa da wuraren kwana, sabo da haka ne, sun rage gajiyata, na gamsu da hakan.'
1 2
|