Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 19:34:50    
Bari mu kalli gasannin Olympic na nakasassu kamar yadda ya kamata

cri

"Za mu yi namijin kokarinmu a dukkan gasanni domin neman kyawawan maki. A waje daya kuma, gasar wasannin Olympic ta nakasassu wani gagarumin biki ne da ke cike da farin ciki da jituwa. Za a iya jin dadin wasannin motsa jiki na nakasassu."

Marc Ledoux, wani dan wasa na kasar Belgium da ya samu lambar azurfa a gun gasar wasan Pingpong a gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Athens ta shekara ta 2004 ya gaya wa wakilinmu cewa, wannan ne karo na uku da ya zo kasar Sin. A 'yan kwanakin da suka gabata, ya kalli gasar wasannin Olympic ta Beijing ta hanyar kallon talabijin. 'Yan kallo na kasar Sin sun burge shi sosai.

"Ina tsammani gasar wasannin Olympic ta Beijing tana da kyau kwarai. Masu shirya wannan gasa sun bayar da gudummowarsu kwarai da gaske. Ina fatan gasar wasannin Olympic ta nakasassu za ta zama wani wurin da 'yan wasa na kasashen duniya su yi gasa a tsakaninsu cikin adalci. Kuma dukkan 'yan wasa za su iya yin kokarinsu domin jin dadin wasannin motsa jiki." (Sanusi Chen)


1 2