Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 19:34:50    
Bari mu kalli gasannin Olympic na nakasassu kamar yadda ya kamata

cri

Lokacin da ake kusantowar gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, mazauna birnin Beijing sun yi kokari sosai wajen sayen tikitocin gasannin Olympic ta nakasassu. Har ma an riga an sayar da dukkan tikitocin gasannin da za a yi a filin motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu" da dakin wasannin ninkayya na kasar, wato Water Cube.

Muhimmiyar ma'anar shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ita ce, shigar da jama'a a cikin gasannin motsa jiki baki daya, wannan ya fi wasannin motsa jiki muhimmanci. Mr. Zhao Jihua, mai ba da shawara kan aikin horaswa kan gasannin wasannin motsa jiki na Olympic ya dade yana kula da wasannin motsa jiki na nakasassu, kuma ya taba shugabancin nakasassu da su shiga gasannin Olympic na nakasassu har sau 4. Ya gaya wa wakilinmu cewa, ya kamata a zura ido kan wasannin motsa jiki na nakasassu da tunanin mutumtaka kamar yadda ya kamata.

"Na kan yi mu'ammala da abokai nakasassu na kasar Sin da na sauran yankunan duniya. Ina ganin cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa nakasassu suka shiga gasannin Olympic shi ne suna son bayyana fatan da ke kasancewa a cikin zukatansu ta hanyar bayyana karfin kasancewarsu a duniya. Wannan fata shi ne 'dalilin da ya sa na yi wasannin motsa jiki shi ne ina son gaya maka, ni da kai, dukkanmu dan Adam ne da ke kasancewa a nan duniya. Kada ka zura idonka kan abubuwan da ban iya yi ba, ya kamata ka zura idonka kan abubuwan da na iya yi'."

A ganin Deng Pufang, shugaban zartaswa na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing, a wajen mutane da ba na nakasassu ba, tunanin mutumtaka shi ne girmamawa da fahimtar juna, wato girmama nakasassu kamar yadda yake girmama kansa. Mr. Zhao Jihua ya ce, "Gasar wasannin Olympic ta nakasassu wata gasar Olympic ta nakasassu ce da ke cike da farin ciki. Wasanni da yawa wasannin motsa jiki ne masu ban sha'awa da ke cike da farin ciki. A hakika dai, a gun gasannin Olympic na nakasassu, ban iya tunawa da wadanda suka samu lambobin zinariya ba, amma na iya tunawa da halin farin ciki da abokai nakasassu suke ciki lokacin da suke shiga wasannin motsa jiki. Sun kuma bayyana iyawarsu ta musamman kan wasannin motsa jiki. Suna zama a nan duniya ne kamar yadda muke zama a nan duniya."

Kungiyar wakilan wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Sin wadda za ta shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing tana kunshe da 'yan wasanni fiye da dari 3. Za su shiga dukkan gasanni 20 na gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Lokaci da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Wang Xinxian, shugaban kungiyar wakilan wasannin motsa jiki na nakasassu ta kasar Sin ya bayyana cewa, ba ma kawai 'yan wasa nakasassu za su yi kokari kan gasanni iri iri ba, har ma za su ji dadin wasannin motsa jiki.

1 2