Yanzu, mahaukaciyar guguwa ta Gustav ta riga ta sanya an dakatar da sana'o'in man fetur da ke yankin tekun Mexico. A ran 31 ga watan Agusta, an riga an rufe ayyukan samar da man fetur da yawansu ya kai kashi 96 cikin kashi dari da ayyukan samar da man gas da yawansu ya kai kashi 82 cikin kashi dari da muhimman tsare-tsaren jigilar makamashi. A waje daya kuma an riga an janye ma'aikata daga yawancin dakalin hako man fetur. Kamfanonin da aka rufe ayyukansu na samar da man fetur a yankin tekun Mexico sakamakon wannan mahaukaciyar guguwa suna kunshe da kamfanin hako man fetur na Britaniya, wato BP da kamfanin Chevron da kamfanin ConocoPhillips da kamfanin Exxon Mobil. Wani sabon rahoton nazari da kasar Amurka ta bayar ta nuna cewa, mai yiyuwa ne yawan gangunan man fetur da za a hako zai ragu da ganguna a kalla miliyan 1 da dubu dari 2 a kowace rana. Yawan man gas da za a hako shi kuma zai ragu da kashi 40 zuwa kashi 50 daga cikin kashi dari. Sabo da haka, manazarta sun yi hasashen cewa, mai yiyuwa ne mahaukaciyar guguwa ta Gustav za ta sanya farashin man fetur a kasuwa ya karu fiye da dalar Amurka 10 ga kowace ganga. Kuma zai zama wani kalubale mai tsanani daban da kasar Amurka ke fuskanta a fannin makamashin man fetur bayan mahaukaciyar guguwa da ta auku a shekara ta 2005.
Sannan kuma, manazarta sun nuna cewa, farashin man fetur yana hauhawa baki daya a cikin shekarar da muke ciki, bayan da farashin man fetur na kowace ganga ya wuce dalar Amurka dari 1 a kasuwar cinikin man fetur ta New York a farkon shekarar da muke ciki, yana ta samun hauhawa cikin sauri. Kuma a ran 11 ga watan Yuli, ya kai dalar Amurka 147.27 ga kowace ganga. Amma bayan wannan rana, farashin man fetur ya soma samun raguwa cikin sauri sakamakon dalilai iri iri. Mai yiyuwa ne mahaukaciyar guguwa ta Gustav za ta sanya farashin man fetur ya tashi ko ya sauka sosai. (Sanusi Chen) 1 2
|