Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-02 18:15:33    
Mahaukaciyar guguwa ta Gustav tana kawo tasiri ga farashin man fetur

cri

A ran 1 ga watan Satumba, lokacin da karfin mahaukaciyar guguwa ta Gustav da ta sauka a kasar Amurka ya ragu, a bayyane ne farashin man fetur da ya taba samun hauhawa sosai ya kuma ragu. Amma yanzu, bangarori daban daban suna mai da hankulansu sosai kan wannan mahaukaciyar guguwa. Manazarta sun nuna cewa, mahaukaciyar guguwa ta Gustav ta riga ta zama muhimmin dalilin da ke kawo tasiri ga farashin man fetur a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. Mai yiyuwa ne za ta sanya farashin man fetur ya tashi ko ya sauka sosai.

A ran 31 ga watan Agusta, kasar Amurka ta rufe kusan dukkan ayyuka da na'urorin samar da man gas da man fetur da ke yankin tekun Mexico, wani muhimmin sansanin samar wa kasar Amurka man fetur da man gas sakamakon bala'in mahaukaciyar guguwa. Wannan mahaukaciyar guguwa da ake kiranta "mahaukaciyar guguwa ta karnin da ake ciki" ta shafi dukkan yankunan Carribean kafin ta sauka a kasar Amurka, inda ta haddasa mutuwar mutane fiye da 80.

Ana mai da hankali sosai kan mahaukaciyar guguwa sabo da ana ganin cewa, mai yiyuwa ne wannan mahaukaciyar guguwa ta Gustav za ta kawo illa sosai ga ayyukan samar da man fetur da man gas da kamfanonin sinadarin man fetur na kasar Amurka da ke yankin tekun Mexico. Yankin tekun Mexico muhimmin sansani ne ga kasar Amurka wajen samar da makamashin man fetur da man gas. Yawan man fetur da man gas da ake samarwa a wannan sansani ya kai kashi 25 cikin kashi dari da kashi 15 cikin kashi dari bisa na dukkan man fetur da man gas da kasar Amurka ke samu a kowace rana. Ban da wannan kuma, karfin sinadarin man fetur na wannan sansani ya kai kusan rabi na duk kasar Amurka. Mahaukaciyar guguwa ta Katrina da ta Rita da suka auku yau da shekaru 3 da suka gabata sun rushe dakalin hako man fetur fiye da dari 1 da ke yankin tekun Mexico. Sakamakon haka, yawan man fetur da kasar Amurka ta samu ya ragu da kashi daya cikin kashi 4. An rufe wasu manyan kamfanonin nace sinadarin man fetur har na tsawon wasu watanni. Sakamakon haka, an haddasa hauhawar farashin man fetur a kasuwa cikin sauri sosai.

1 2