Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 18:34:45    
An fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing

cri

A gun bikin kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu da aka gudanar a ran nan, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing, Mr.Liu Qi ya yi fatan alheri ga yawo da wutar wasannin Olympic na nakasassu da za a fara yi, ya ce,"Lokacin da aka kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu a wurin ibada na heaven temple, da sahihiyar zuciya ce muke fatan wutar za ta iya isar da fatan alheri na jama'a ga wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da kuma kulawarsu ga nakasassu, ta hada zukatan jama'a wadanda ba su da nakasa da na nakasassu."

A gun bikin kuma, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya, Philip Craven ya ce,"Nan da kwanaki masu zuwa, ko a gun filayen wasa ko kuma a cikin zamansu na yau da kullum, 'yan wasa nakasassu za su bayyana mana ruhu na musamman na wasannin motsa jiki, kuma wutar za ta zama alama. Bisa wannan ruhu ne, 'yan wasa za su tsallake matsaloli da dama, kuma za su yi kokarin neman samun kyawawan cigaba."

Bisa kidayar da aka yi, an ce, a halin yanzu dai, akwai nakasassun da yawansu ya kai miliyan 650 a duk duniya, kuma a lokacin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, 'yan wasa nakasassu fiye da 4,000 tare da malamansu sama da 2,500, da kuma jami'ansu, wadanda suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 150, za su shiga wasannin, sabo da haka, wasannin Olympic na nakasassu na Beijing za su fi samun hallarar kasashe da yankuna a tarihi.

A gun bikin kunna wutar, shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin, Mr.Deng Pufang ya bayyana fatansa na alheri ga wasannin Olympic na nakasassu, ya ce, "wasannin Olympic na nakasassu biki ne na jama'ar duniya baki daya, haka kuma kasaitaccen biki ne da 'yan adam suka kawar da bambamcinsu da kuma zauna lafiya da zama jituwa da juna, muna alla-alla ga zuwansa, bisa tutar 'duniya daya, mafarki daya ne', muke son yin kirari ga zaman lafiya da cigaba da zumunci da jin kai tare da jama'ar duniya."(Lubabatu)


1 2