Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-28 18:34:45    
An fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing

cri

Yau 28 ga wata da safe, a wurin ibada da ake kira heaven temple da ke nan birnin Beijing, an kunna wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, kuma firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ya sanar da fara mika wutar a hukunce.

Bisa wakar kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ne, madam Jiang Xintian, wata kurma mai gabatar da shirye-shirye a kungiyar wasannin fasaha ta nakasassu ta kasar Sin, ta kunna wutar wasannin Olympic ta nakasassu bisa wani madubi. Daga baya, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ya sanar da cewa, "Yanzu an fara mika wutar wasannin Olympic na nakasassu na Beijing."

Nan da kwanaki 9 masu zuwa, bisa hanyoyi biyu ne, wato hanyar 'Sin ta zamani' da kuma hanyar 'Sin ta gargajiya', za a mika wutar wasannin Olympic na nakasassu a birane 11 na kasar Sin, ciki kuwa har da Luoyang da Nanjing da Shenzhen da Shanghai da Qingdao da Changsha da sauransu, kuma wutar za ta isa babban filin wasan kasar Sin da ake kira 'shekar tsuntsu' a ranar 6 ga watan Satumba mai zuwa, wato ranar da za a fara wasannin Olympic na nakasassu, inda za a kunna babbar wutar yola ta wasannin Olympic na nakasassu a wannan karo.


1 2