Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 11:58:19    
Cibiyar wasannin ruwa ta kasar Sin

cri

A matsayin daya daga cikin gine-ginen da ke kasancewa alamun taron wasannin Olympic na Beijing, cibiyar wasannin ruwa ta kasar Sin, wadda ake kira wurin tattara ruwa, wato Water Cube a Turance, za ta bakunci gasannin ninkaya da tsunduma cikin ruwa daga katako da salon iyo da kuma wasan kwallon ruwa wato water polo a lokcin Olympic na shekarar 2008, tana kuma daya daga cikin filayen wasa mafi muhimmanci a gun taron wasannin Olympic na Beijing. Wannan kyakkyawan gini mai launin shudi na zauna a arewacin birnin Beijing. Har kullum an mayar da shirin zayyana shi tamkar daya daga cikin shirye-shirye mafi ban sha'awa a fannin zayyana filayen wasa na taron wasannin Olympic na Beijing.

Wannan cibiya na da kusurwoyi 4, ta yi kama da wani akwati. Amma babban dalilin da ya sa ta fi jawo hankulan mutane shi ne domin fatarta, wato abubuwan kumfa masu launin shudi da aka shafa a waje da ita. A kan irin abubuwan musamman kuwa an yi zane-zanen da suka yi kama da halittun ruwa. Ban da wannan kuma, mutane na iya kallo ta ko wace fuskar irin wadannan abubuwan musamman. In an hango shi daga nesa, sai ka ce wani wurin da aka lullube shi da dimbin kumfa masu launin shudi. Musammam ma, in dare ya yi duhu, bayan da aka kunna futilu a cikin wannan cibiya, haske na fitowa ta irin wadannan abubuwan musamman masu launin shudi. In wani ya tsaya a waje da cibiyar, sai ka ce, yana more idonsa da wnai kyakkyawan lu'ulu'u mai launin shudi, wanda aka yi kallo ta ko wace fuska.

Bugu da kari kuma, a cikin wannan cibiyar wasannin ruwa, an shafa irin wadannan abubuwan musamman a jikin bango. Mutane na iya ganin irin wadannan abubuwan musamman da aka yi zane-zanen halittun ruwa a kansu a cikin tsabataccen ruwa a wurin ninkaya, saboda haka 'yan kallo sun yi kama da shiga duniyar halittun ruwa. Kallon gasannin ninkaya a nan na da ban mamaki da sha'awa. A cikin wannan cibiya, an samar da kujeru dubu 17 na 'yan kallo, a ciki kuma, wasu dubu 6 na din din din, za a samar da karin kujeru dubu 11 na wucin gadi, wadanda za a cire su bayan taron wasannin Olympic na Beijing.


1 2