Ban da wannan kuma birnin Beijing ta yi la'akari da abubuwa da dama. Alal misali,a yarda makafi na tafiya a wuraren taruwar jama'a tare da karnukansu,haka kuma an shirya injuna domin makafi a filaye da dakunan wasanni da sauran kayayyakin musamman domin su.
Mataimakiyar shugabar zartaswa ta kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing Madam Tang Xiaoquan ta bayyana cewa da akwai ma'aikatan musamman dari shida da masu sa kai dubu dari uku da za su ba da hidima ga 'yan wasa nakasassu fiye da dubu hudu da metan da suka zo daga kasashe da bangarori 148 na duniya, birnin Beijing ta yi iyakacin kokarinta domin tabbatar da gasar wasannin ta Olympics ta Beijing ta nakasassu ta samu nasara kamar yadda gasar Olym;pics ta Beijing ta yi.(Ali) 1 2 3
|