Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 12:30:55    
An kammala aikin share fage gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Daga cikin ayyukan share fage,abin da ya fi daukar hankalin mutane shi ne gyara wasu abubuwan da ke cikin filaye da dakunan da ba su dace da bukatun nakasassu ba. Bisa labarin da mataimakiyar shugaban mai zartaswa na kwamitin shirya gasar Olympics na Beijing Madam Tang Xiaoquan ta bayar, an ce ayyukan share fage na tafiya daidai a duk filaye da dakunan wasa da aka shirya domin 'yan wasa nakasassu halin yanzu.

"kayayyakin dake cikin filaye da dakunan wasannin da kuma hanyoyin da aka tanada domin 'yan wasa nakasassu sun kai matsayin da gwamnatin kasar Sin tsaida,cibiyar wasannin ta kasa da sauran filayen wasanni guda hudu dukkansu sun kai matsayi na duniya. A halin yanzu a dukkan filaye da dakunan wasannin da za a yi gasanni na nakasassu,an shiga jarrabawa. Ana cikin shirin bincike kayayyakin da aka shimfida da kuma shirye shiryen da aka tsara domin 'yan wasa nakasassu na aiki daidai ko ba daidai ba,idan a gano matsala a warware ta nan take.

Bisa labarin da muka samu, an ce da akwai filaye da dakunan wasanni 20 da aka tanada domin 'yan wasa nakasassu na gasar Olympics ta Beijing ta nakasassu, da filaye da dakuna shida na ba da horo,dukkansu sun yi aiki ne a yayin da ake gasar Olympics ta Beijing. Ban da wannan kuma an tanadi asibitoci 22 domin 'yan wasa nakasassu da otel otel 16. dukkansu an yi musu kwaskwarima ta yadda 'yan wasa nakasassue za su samu sauki wajen samun hidima.

Yayin da aka yi gasar Olympics ta Beijing,an samar da hidima ga mutanen ke bukata a birnin Beijing, an kuma samu yabo daga bangarori daban daban. Domin kawo sauki ga 'yan wasa nakasassu wajen kallon wasanni da zama,birnin Beijing ya yi namijin kokarin tabbatar da zirga zirgar motocin gari yadda ya kamata.Tang XiaoQuan ta ci gaba da cewa

" mun sanya kokari wajen gyara hanyoyin tafiya da sauran kayayyaki domin kawo sauki ga nakasassu a lambunan sha iska da otel otel; da masaukan baki da kuma bankuna. Mun bude hanyoyi 16 na musamman domin motocin gari a gasar olympics ta nakasassu da motoci dari hudu domin su.An shimfida tasoshi 123 a gefunan hanyoyi 8 na mototcin gari, a kalla dai a kowace tasha da akwai mashigi daya da nakasassu da ke amfani da kekuna masu kafaffuwa ke iya shiga da fita.

A sa'I daya kuma birnin Beijing ta shirya wani gwanon motocin haya musamman domin nakasassu yayin da ake gasar Olympics ta nakasassu a nan birnin Beijing.


1 2 3