Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-19 17:46:30    
Gasar Olympic, sabuwar alama ce da ke bayyana yadda kasar Sin take hada kanta da sauran kasashen duniya

cri

Jama'a masu sauraro, wannan ne ainihin tunani na taken "duniya daya, mafarki daya" da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana wa duniya. A cikin wakar da aka rubuta domin wannan gasar Olympic ta Beijing musamman. Ana rera cewa "Kai da ni, ana hada zukatanmu tare, muna zama a kauyen duniya daya. Kuma mun yi tafiya har tsawon kilomita dubu 1 domin haduwa da juna a Beijing." Wannan wakar gasar Olympic ta Beijing tana bayyana kyakkyawan fata na "duk wanda ke zama a duniya iyalai ne".

Jama'a masu sauraro, a hakika dai, bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje a kasar Sin cikin shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin ta riga ta gane cewa, bude kofa da hada kanta da sauran kasashen duniya wajabtacciyar hanya ce da kasar Sin ta bi domin neman cigaba da bunkasuwa. Ko shakka babu, gasar Olympic ta Beijing wani babban cigaba ne da kasar Sin ta samu lokacin da take hada kanta da sauran kasashen duniya. Kuma wannan gasar Olympic za ta zama wata alamar da ke bayyana cewa kasar Sin za ta hada kanta da sauran kasashen duniya daga dukkan fannoni.  (Sanusi Chen)


1 2