A kwanan baya, wata kafar watsa labaru ta kasar Sin ta yi sharhi kan gasar Olympic ta shekara ta 2008 ta Beijing da ake yi yanzu, cewar "tabbas ne gasar Olympic ta Beijing za ta zama wata alama, wato, kafin gasar Olympic, kasar Sin ta hada kanta da sauran kasashen duniya ta fuskar tattalin arziki, amma tun daga yanzu, tana hada kanta da sauran kasashen duniya a fannonin al'adu da zaman al'umma."
Yau da shekaru 7 da suka gabata, lokacin da Mr. Juan Antonio Samaranch, wato shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa na wancan lokaci ya sanar da cewa, birnin Beijing ya samu izinin shirya gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a shekara ta 2008. Lokacin da wannan kuduri yake kawo wa jama'ar kasar Sin farin ciki, ya fi kawo wa kasar Sin wani nauyi.
Gasar wasannin Olympic gaggarumin biki ne a gare duk duniya. Kasar Sin ta nemi izinin shirya gasar wasannin Olympic, ba ma kawai tana son daga matsayinta a duniya ba, har ma tana bayar da gudummowarta ga wasannin Olympic, kuma tana sauke nauyin da duk al'ummomin duniya suka yi mata. A cikin shekaru 7 da suka gabata, kasar Sin ta yi kokari sosai wajen shirya wata gasar Olympic cikin nasara a cikin hali mai yakini.
Bayan shekaru 7, a gun wani taron manema labaru da aka yi a jajibirin bikin kaddamar da gasar Olympic ta Beijing, Mr. Jacques Rogge, shugaban yanzu na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya ce, "Tabbas ne kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ba zai yi da-na-sani ba kan kudurin bai wa Beijing ikon shirya gasar Olympic. A lokacin da ake shiga ranar 8 ga watan Agusta, gasar wasannin Olympic da ke da karfin jawo hankulan mutane sosai da ayyukan shirya wannan gasar da aka yi za su mamaye dukkan cece-ku-ce."
Idan an ce, kokarin da kasar Sin ta yi yana bayyana yadda ita da kanta ne take sauke nauyin da ke bisa wuyanta da ke da nasaba da duk duniya, wasu tunani da ra'ayoyin da aka tabbatar a gun gasar Olympic ta Beijing sun bayyana yadda kasar Sin take sharhi kan wasannin Olympic da huldar da ke tsakaninta da sauran kasashen duniya, kuma suna bayyana yadda kasar Sin take amincewa da wasu tunanin zaman rayuwa da ke shafar duk bil Adam.
"Taken 'duniya daya, mafarki daya' yana bayyana ruhun Olympic sosai, kuma yana bayyana makasudin gasar Olympic ta Beijing. Wannan take yana bayyana fatanmu cikin sahihanci, wato jama'ar kasar Sin tana son kara yin musanye-musanye da hadin guiwa a tsakaninsu da jama'ar sauran kasashen duniya bisa ruhun Olympic domin bude sabon shafi na wasannin Olympic na kasa da kasa da raya wata kyakkyawar makoma ga bil Adam."
1 2
|