Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-18 12:10:04    
Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru

cri

Dadin daddawa, kammala bikin mikawa ya bayyana cewa wani muhimmin aiki daban ya fara.shi ne tsungunar da mazaunan tsibirin Bakassi. Da akwai mazauna kimani dubu dari uku a tsibirin Bakassi,kashi fiye da casa'in bisa dari mutane ne na Nijeriya.Gwamnatin Nijeriya ta fara tsungunar da mazaunan a jihohin kusa da tsibirin.amma rumfunan da aka kafa ba su iya biya bukatun mazaunan da suka yi kaura ba, manyan ayyukan da ke cikin jihohi na kusa a baya suke,masu neman kaura da yawa sun sha wahala wasunsu ba su iya samun isashen abinci da sutura,wasunsu kuma suna kwana a waje. sauro ya kan cije su har ma sun kamu da cutar malaria,ba su iya samun magani cikin lokaci ba.

Masu binciken al'amuran suna masu ra'ayi cewa Nijeriya da Kamaru sun nuna halayyar nagari mai ban girma na girmawa juna da hadin kai cikin aminci wajen warware matsalar mallakar tsibirin Bakassi,duk da haka bangarori biyu sn yi biris da ainihin moriyar mazaunan tsibirin Bakassi. Ga shi a yau an daidaita matsalar mallakar tsibirin Bakassi,kamata ya yi kasashen nan biyu su kara kokarinsu da zuciya daya,su kare moriyar mazaunan tsibirin. Ban da wannan kuma kamata ya yi Majalisar Dinkin duniya da sauran kungiyoyin duniya sub a da Karin taimako domin tsungunar da mazaunan tsibirin.


1 2